Rukunan Sallah Da Wajibanta Da Sunnoninta

40334
Rukunan sallah su ne

Vangarorinta na asali waxanda take samuwa da su, ta yadda baya halatta a bar su a kowane irin yanayi, basa saraya da gangan ko da mantuwa sai dai a halin gazawa.

Na farko : Rukunan Sallah

1 – Niyya

2 – Tsayuwa a sallar farillah idan da iko.

3 – Kabbarar Harama

4 – Karatun Fatiha

5 – Ruku’u

6 – Daidatu idan an xago daga ruku’u

7 – Sujjada akan gavvai bakwai

8 – Zama tsakanin sujjadu biyu

9 – Zama don yin tahiyar qarshe

10 – Karanta tahiyar qarshe

11 – Salati ga Annabi (S.A.W) a tahiyar qarshe

12 – Sallama

13 – Nutsuwa a cikin dukkan rukunai

14 – Jerantawa tsakanin rukunai.

Wanda ya bar rukuni daga cikin rukunai me zai aikata?

1 – Wanda duk ya bar rukuni da gangan sallarsa ta vace, kuma wajibi ne ya ramata.

2 – Wanda ya bar rukuni da mantuwa, to xayan biyu ne :

A – Ya zama bai tuna ya bar wannan rukunin ba, har sai da ya zo wajensa a raka’a mai zuwa, to anan ba zai lissafa da waccan raka’ar ba wadda ya bar rukuni a cikinta ba, sai ya mayar da wannan raka’ar da yake cikinta a matsayin waccan da ya yi mantuwar a cikinta, sannan sai ya yi sujjadar rafkanuwa [Duba yadda ake sujjadar rafkanuwa a babin sujjadar godiya ga Allah da rafkanuwa da sujjadar karatun Alqur’ani, shafi na 64 – 66].

Misalin haka : Mutum ne ya tuna yayin da yake cikin raka’a ta biyu wajen karatun fatiha cewa ya manta karatun fatiha a raka’a ta farko, to anan zai mayar da wannan raka’a ita ce raka’ar farkonsa, ya qyale wadda ta gabata.

B – Ya tuna cewa ya manta rukuni a cikin raka’a, gabanin ya kai wajen irinsa a raka’a ta gaba, to anan ya wajaba da ya tuna ya koma baya ya zo da wannan rukunin.

Misalinsa : Mutum ya manta bai yi ruku’u ba, ya yi sujjada yayin da ya gama karatunsa, yana cikin sujjadar sai ya tuna cewa bai yi ruku’u ba, to anan wajibi ne ya tashi ya yi ruku’a, sannan ya cika sallarsa.

Abu na biyu : Wajiban Sallah

Wajiban Sallah su ne

Abubuwan da sujjadar rafkanuwa take gyara su, idan an manta kuwa sun saraya.

1 – Kabbarorin tashi daga wata siffa zuwa wata siffa.

2 – Faxin «Subhana Rabbiyal Azeem” a ruku’u.

3 – Faxin “Sami’al Allahu Liman Hamidahu” ga liman da wanda yake shi kaxai, amma ba a shar’anta hakan ba ga mamu.

4 – Faxin “Rabbana Walakal Hamdu” a wajen xagowa daga ruku’u.

5 – Faxin “subhana Rabbiyal A’ala”a a cikin sujjada.

6 – Faxin “Rabbig Fir li” a tsakanin sujjadu biyu

7 – Zaman tahiyar farko

8 – Tahiyar farko

Wanda ya bar wajibi daga wajiban sallah me zai yi?

1 – Wanda ya bar wajibi da gangan sallarsa ta vace, kuma wajibi ne ya ramata.

2 – Wanda ya bar wajibi da mantuwa, sallarsa ta yi, sai dai zai yi sujjada biyu na rafkanuwa kafin ya yi sallama.

Na uku : Sunnonin Sallah

Duk abin da baya cikin sharuxxan sallah ko rukunanta ko wajibanta na daga abin da aka ambata a siffar sallah to wannan abu ne sunna ne, barin wannan abu bai zai yi tasiri ba a ingancin sallah, barinsa baya wajabta sujjadar mantuwa.

Sunnonin Sallah iri biyu ne :

Na farko : Sunnonin Da Ake Faxa

Suna da yawa, daga cikinsu akwai :

1 – Addu’ar buxe sallah, ita ce addu’ar da ake faxa kafin karatun fatiha.

2 – Neman tsari daga wajen Allah, shi ne faxin «A’uzu Billahi Minash Shaixanir Rajiim”.

3 – Yin Bismillah, ita ce faxin “Bismillahir Rahmanir Rahim”.

4 – Abin da ya qaru akan xaya a tasbihin ruku’u da sujjada.

5 – Abin da ya wuce xaya daga faxin “Rabbig Fir li” a tsakanin sujjadu biyu.

6 – Abin da ya qaru akan faxin “Rabbana Walakal Hamdu” bayan xagowa daga ruku’u.

7 – Abin da ya qaru akan karatun fatiha.

Na biyu : Sunnonin Da Ake Aikatawa

Suna da yawa, daga cikinsu akwai :

1 – Xaga Hannaye tare da kabbarar harama, da yayin ruku’u, da xagowa daga gare shi, da yayin tsayuwa zuwa raka’a ta uku.

2 – Xora hannun dama akan na hagu a yayin tsayuwa kafin ruku’u.

3 – Kallon wurin sujjada

4 – Nisantar da hannaye daga ciki da gefe yayin sujjada

5 – Zama yana mai shimfixa qafarsa da dama, kuma ya sanya ‘yan yatsunta suna kallon alqibla, yana mai shimfixa kafar ta hagu a zaune a kanta.

Wannan zama sunna ne a dukkan zaman sallah banda na tahiyar qarshe a sallar da tafi raka’a biyu.

6 – Zaman Harxe : shi ne zaman da ake kafe qafar dama, ana mai sanya ‘yan yatsu suna kallon alqibla, a sanya qafar hagu qarqashin qwabrin dama da fito da ita ta vangaren dama, da zama akan mazaunai ana mai dogara aka hagu.

A sunnanta wannan zama a tahiyar qarshe a sallar da ta wuce raka’a biyu.

Zaman Harxe
Zaman Shimfixe


Tags: