Kiran Sallah Da Iqama

59327

Bayanin kiran sallah da iqama

Kiran Sallah shi ne

Sanar da shigar lokacin sallah ta hanyar wani zikiri kevantacce.

Iqama ita ce

Sanar da tsayuwar sallah da wani zikiri kevantacce

Hukuncin Kiran Sallah Da Iqama

1 – A kan jama’a :

kiran sallah a yayin sallolin farillah guda biyar fardu kifaya ne [ Fardu Kifaya : shi ne wajibin da idan waxansu suka yi, sun xaukewa sauran.], (wato in wasu suka yi sun xauke wa wasu) a halin tafiya da zaman gida, saboda kiran sallah da iqama suna cikin ayyukan musulunci na zahiri, don haka baya halatta a daina yin su.

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “idan lokacin sallah ya yi, xayanku ya yi kiran sallah, sannan babbanku ya yi muku limanci” [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.]

2 – Dangane da mutum xaya :

kiran sallah sunna ne. An karvo daga Uqbatu xan Amir – Allah ya yarda da shi – ya ce, na ji Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ubangijinka yana mamakin makiyayin dabbobin a kan dutse, da yake yin kiran sallah ya yi sallah, sai Allah ya ce, “Ku kalli bawana wannan, yana kiran sallah, ya tsaida sallah, yana jin tsorona, na gafarta wa bawana, na shigar da shi Aljannah” [Nasa’i ne ya rawaito shi.].

HIKIMAR KIRAN SALLAH

1 – Shelanta shigar lokacin sallah da wurin da za a tsaida ta.

2 – Kwaxaitarwa a kan yin salla a cikin Jam’i.

3 – Faxakar da gafalallu waxanda suka sha’afa, da tunatar da waxanda suka manta, don yin sallah wadda ita ce mafi girman ni’ima.

Yaushe aka shar’anta kiran sallah da dalilin hakan?

An shar’anta kiran sallah a shekarar farko bayan hijira, dalilin haka kuwa shi ne : Yayin da aka samu buqatar sanya wata alama da kowa zai gane cewa lokacin sallah ya yi, sai musulmi suka yi shawara a kan hakan, da dare ya yi, sai Abdullahi xan Zaid ya yi mafarki ya ga wani mutum yana xauke da qararrawa, sai ya ce da shi «Zaka sayar min da wannan qararrawar?» sai mutumin ya ce masa, «Me zaka yi da ita?» Sai ya ce, «Zamu yi kiran sallah da ita ne», sai mutumin ya ce, «Ba na nuna maka abin da ya fi wannan alheri ba?» Sai Abdullahi ya ce, «Eh, nuna min» Sai ya koya masa kiran sallar da ake yi, sannan ya koya masa iqama». [Darimi ne ya rawaito shi. ]

Abdullahi ya ce, «Da gari ya waye, na zo wajen Manzon Allah (S.A.W) na ba shi labarin abin da na gani» sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Haqiqa wannan mafarki ne na gaskiya – insha Allahu – je ka kai da Bilal ka faxa masa (kiran sallar) saboda shi ya fika daxin murya” [Abu Dawud ne ya rawaito shi.].

Falalar Kiran Sallah

1 – Duk wanda muryar mai kiran sallah ta kai masa, zai masa shaida a wajen Allah ranar alqiyama. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Aljani ko mutum ko wani abu daban, babu wanda zai ji muryar mai kiran sallah daga cikinsu, face sai ya yi masa shaida ranar Alqiyama” [Bukhari ne ya rawaito shi.].

2 – Mutane da sun san abin da yake cikin kiran sallah na falala da sun yi rige-rige zuwa gare shi, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Da mutane sun san abin da yake cikin kiran sallah da sahun farko, sannan a ce ba za su same su ba sai sun yi quri’a a kai, da sun yi” [Bukhari ne ya rawaito shi.]

Sharuxxan Ingancin Kiran Sallah

1 – Wanda zai yi shi ya zama musulmi ne, namiji, mai hankali.

2 – Kiran sallar ya zama a jere.

3 – Ya zama mai bin juna, kada a samu yanke wa mai girma tsakanin kalmominsa.

4 – Ya kasance an yi shi yayin da lokacin sallah ya shigo.

Sunnonin Kiran Sallah

1 – Fuskantar alqibla.

2 – Tsarkakar mai kiran sallah daga kari guda biyu.

3 – Waiwaya wa dama da hagu, a lokacin da ya zo faxar «Hayya alal Salah, Hayya alal Falah”

4 – Mai kiran sallah ya sanya xan yatsansa manuniya a cikin kunnuwansa.

5 – Mai kiran sallah ya zama yana da murya mai daxi mai qarfi.

6 – Rera kiran sallah da nutsuwa a cikinsa.

‘yan yatsun Manuniya a cikin kunne

Yadda Ake Kiran Sallah

1 – Yadda ake kiran sallah shi ne, “Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Ashhadu An La’ilaha ilal Lah, Ashhadu an la’ilaha ilal lah, Ashhadu anna Muhammadan Rasulullah, Ashhadu anna Muhammadan Rasulullah, Hayya alal Salah, Hayya alal Salah, Hayya alal falah, Hayyah alal falah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, La’ilaha ilal Lahu” [Muslim ne ya rawaito shi].

2 – Yadda ake Iqama : “Allahu Akbar, Allahu Akbar, Ashhadu An La’ilaha ilal Lah, Ashhadu anna Muhammadan Rasulullah, Hayya alal Salah, Hayya alal falah, Qad Qamatus Salatu, Qad qamatus Salah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, La’ilaha ilal Lahu”.

Abin Da Ake Son Wanda Ya Ji Kiran Sallah Ya Yi

1 – Ya faxi irin abin da mai kiran sallah ya faxa, sai dai wajen faxin “Hayya alal Salah, Hayya alal Falah” sai ya ce, “La Haula wala Quwwata Illa Billah” [Bukhari ne ya rawaito shi.].

2 – Bayan an gama kiran sallar ya ce, “Ashhadu an la’ilaha wahdahu, la sharika lahu, wa anna Muhammadan Abduhu Wa Rasuluhu, Raditu billahi Rabban, Wa bi Muhammadin Rasulah, Wa bil islami dinan” [Muslim ne ya rawaito shi].

3 – Ya yi wa Annabi (S.A.W) salati bayan gama kiran sallar, sannan ya ce, “Allahumma Rabba Hazihid Da’awatit Tammati, Wassalatil Qa’imati, Ati Muhammadanil Wasilata wal Fadilah, Wab’ashu maqaman mahmudanil lazi wa’addahu” [Bukhari ne ya rawaito shi].

4 – Ya yi wa kansa addu’a tsakanin kiran sallah da iqama, saboda addu’a a wannan lokacin ba a mayar da ita, saboda faxin Manzon Allah (S.A.W) “Haqiqa addu’a tsakanin kiran sallah da iqama ba a mayar da ita” [Ahmad ne ya rawaito shi].

Wasu Daga Cikin Hukunce-Hukuncen Kiran Sallah Da Iqama

1 – Ana wadatuwa da kiran sallah xaya, yayin haxa sallar azzahar da la’asar, amma ana yi wa kowace iqamarta.

2 – Idan aka yi iqama, sannan aka jinkirta tayar da sallah, to babu buqatar sai an sake iqama idan za a yi sallar.

3 – Mai kiran sallah ya kiyayi yin kuskure a cikin lafuzzan kiran sallah, daga cikin irin waxannan kurakuran akwai :

A) faxin «Aaallahu Aaakbar» (wato ya yi ja akan alif xin farko na sunan Allah da alif xin farko na Akbar) kamar yana tambaya kenan.

B) Faxin «Allahu Akbaar» wato ya yi ja akan ba’un xin Akbar».

C) Faxin «Allahu Wa Akbar» ya qara wawun.

4 – Idan an tayar da sallah to baya halatta a fari yin nafila a lokacin, idan ya fara nafilar sannan aka ta da sallah to sai ya gama nafilarsa idan abin da ya rage masa kaxan ne, idan kuwa da yawa, to sai ya yanke ta – ba sai da sallama ba – ya bi liman a yi farillah.

5 – Kiran sallar yaro wanda yake bambance abubuwa ya inganta.

6 – An shar’anta yin kiran sallah da iqama yayin da za a rama sallar da ta wuce, saboda barci ko mantuwa, saboda abin da ya tabbata daga Annabi (S.A.W) lokacin da ya yi barci shi da sahabbai, ba su yi sallar asuba ba har rana ta vullo, sai Manzon Allah “(S.A.W) ya umarci Bilal ya yi kiran sallah, sannan suka yi alwala, suka yi raka’a biyu nafilar asuba, sannan ya umarci Bilal ya yi iqama, Manzon Allah (S.A.W) ya yi musu limancin sallar asuba” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

7 – Kada wanda yake cikin masallaci ya fita bayan an yi kiran sallah sai dai in da wani uzuri, saboda abin da Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya rawaito ya ce, “Manzon Allah (S.A.W) ya umarce mu idan kuna cikin masallaci, aka kira sallah, kada xayanku ya fita har sai an yi sallah” [Ahmad ne ya rawaito shi].

8 – An shar’anta wa mai kiran sallah ya yi qasa-qasa da muryarsa a wajen faxin Ashhadu An la’ilah…da Ashhadu anna Muhammadan.., sannan ya maimata su da qarfi, saboda hakan ya tabbata a sunnah.[Abu Dawud ne ya rawaito shi]

Bai Dace Ba

1 - Karkarya muryaa cikin kiran sallah, da rera shi kamar waqa, ta yadda har za a canza wasu haruffai da wasula, da qarawa da ragewa.

2 – Yin salati da sallama ga Annabi da murya mai qarfi bayan gama kiran sallah.

3 – Faxin «Aqamahal Lahu Wa adamaha» yayin da aka ji an ce «Qad Qamatus salatu» kurum abin da ake so mutum ya maimata ta kamar yadda aka faxe ta.

Kiran Sallar Asuba :

Kiran Sallah biyu aka shar’anta da asuba, na farko kafin shigowar lokaci, na biyu don sanar da cewa lokaci ya shigo saboda a zo sallah, don haka an shar’anta a kiran sallar farko mai kiran sallah ya ce, «Assalatu Khairum Minan Naum» sau biyu, saboda faxin Manzon Allah (S.A.W) «Idan ka yi kiran sallar farko na asuba, ka ce, “Assalatu Khairum minan Naum, Assalatu khairum minan Naum” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].Tags: