Sharuxxan Ingancin Sallah

10717

Abu Na Farko : Shigowar Lokaci

Sallar farillah tana da lokacin da bata inganta kafin shi, ko bayan shi, sai dai ga mai uzuri. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Lalle ne sallah ta kasance akan mumunai farilla ce mai qayyadadden lokaci”. (Annisa’i : 103)

Ma’ana farillace da take da wani lokaci iyakantacce.

- Lokutan Sallah Su ne :

1 – Lokacin Sallar Asuba :

Daga vullowar alfijir na gaskiya wanda shi ne wani fari da yake sama ta vangaren gabas – zuwa vullowar rana.

2 – Lokacin sallar azzahar :

Daga karkacewar rana daga sama zuwa inuwar komai ta yi daidai da shi, bayan inuwar da fito bayan karkacewar rana.

Saboda rana idan ta fito sai ya zama abu yana da inuwa ta vangaren yamma, haka wannan inuwar zata yi ta raguwa duk lokacin da rana ta xaga, har inuwar ta tsaya cak, sannan sai inuwar ta ci gaba da qaruwa, to idan inuwar ta ci gaba da qaruwa, wannan shi ne lokacin karkacewar rana.

3 – Lokacin sallar la’asar :

Daga qarewar lokacin azzahar har zuwa inuwar komai ta zama ninkinsa biyu, bayan inuwar da take lokacin karkacewar rana.

4 – lokacin sallar magariba :

Daga faxuwar rana zuwa vuyan ja-ja xin nan na sama, wanda yake zuwa bayan faxuwar rana.

5 – Lokacin sallar isha :

Daga qarshen lokacin sallar magariba zuwa rabin dare, saboda faxin Manzon Allah (S.A.W) “Lokacin sallar isha zuwa rabin dare na tsakiya” [Muslim ne ya rawaitoshi].

A wannan zamani za a iya sanin lokutan sallah a cikin sauqi ta hanyar kalanda.

Sallar Asuba
Sallar Azzahar
Sallar La’asar
Sallar Magariba
Sallar Isha
Fa’idoji

1 – Wanda ya riski raka’a xaya kafin lokacin sallah ya fita, to ya riski wannan sallah, saboda faxin Manzon Allah (S.A.W) “Wanda ya riski raka’a xaya daga sallah, to ya riski sallah” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

2 – Ya wajaba a rama sallah da wuri idan ta kubce saboda barci ko mantuwa, saboda faxin Manzon Allah (S.A.W) : “Wanda ya manta sallah, to ya sallace ta idan ya tuna ta, babu wata kaffarar ta sai yin hakan” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Abu Na Biyu : Tsarkaka Daga Kari

1 – Tsarkaka daga kari qarami :

Ana tsarkaka xin ne da alwala, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Allah baya karvar sallar xayanku idan ya yi kari, har sai ya yi alwala” [Bukhari ne ya rawaito shi].

2 – Tsarkaka daga kari babba :

Ana tsarkaka xin ne da wanka, saboda faxin Allah mai girma da buwaya : “Idan kun kasance da janaba to ku tsarkaka”. (Al-ma’idah : 6).

Wanda ya tuna ya yi kari alhali yana sallah, ko kuma ya yi karin a cikin sallar, to sallar shi ta lalace, kuma dole ne ya bar sallar ba tare da sai ya yi sallama ba, ya je ya yi tsarki, saboda sallarsa ta yanke ba ta cika ba, ita kuwa sallama ita ce cikar sallah.

Abu Na Uku : Tsarkin Tufafi Da Jiki Da Wuri

1 – Tsarkin tufafi :

saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Kuma tufafinka ka tsarkake su” (Al-muddassir : 4).

Tsarkin tufafi

2 – Tsarkin Jiki :

saboda abin da ya tabbata cewa Manzon Allah (S.A.W) ya wuce ta wajen wasu qabari guda biyu, sai ya ce, “Lallai ana yi musu azaba, kuma ba wani babban abu ba ne ya sa ake musu azaba ba [Baya tsakaka daga fitsari baya nisantarsa, baya kiyaye kansa daga gare shi], shi dai wannan baya tsarkaka daga fitsari (bawali)” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Tsarkin jiki

3 – Tsarkin Guri :

saboda hadisin mutumin qauyen nan da ya yi fitsari a masallaci, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ku qyale shi, ku kwarara guga cike da ruwa a kan fitsarinsa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Tsarkin Wuri

Sallah Da Najasa

Wanda ya yi sallah da najasa bai san da ita ba, ko kuma ya manta da ita, sallarsa ta yi, saboda abin da ya tabbata cewa “Manzon Allah (S.A.W) yana sallah, sai ya cire takalmansa, sai mutane suka cire takalmansu, yayin da Manzon Allah (S.A.W) ya gama, sai ya juyo ya ce, “Me yasa kuka cire takalmanku?” Sai suka ce, “Ya Manzon Allah (S.A.W) mun ga ka cire takalmanka, sai muma muka cire”, Sai ya ce, “Jibrilu ne ya zo ya ce min, “a cikinsu akwai najasa, idan xayanku ya zo masallaci, ya juya takalmansa, ya duba su, idan ya ga najasa a jikinsu to ya goge su da qasa, sannan ya yi sallah da su” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Wanda ya san yana da najasa alhali yana cikin sallah, to wajibi ne ya gusar da ita, sannan ya ci gaba da sallarsa, ya xora a kan abin da ya salllata, saboda hadisin da ya gabata, idan kuwa ba zai iya gusar da ita ba to sallar shi ta lalace.

Qasa Gaba Xayanta Wurin Sallah Ne

Bayan qasa gaba xayansa wurin sallah ne, sallah tana inganta a kanta, Manzon Allah (S.A.W) ya ce,“An sanya min qasa ta zama masallaci da tsarki gare ni, kowane mutum a cikin al’ummata da sallah ta riske shi to ya yi ta (a ko’ina ne)”[Bukhari da Muslim ne ya rawaito shi].

Amma an kevance daga bayan qasa abin da hani ya zo a kansa, kamar sallah a maqabarta, da ban-xaki, saboda faxin Manzon Allah (S.A.W) “Qasa gabaxayanta wurin sallah ne, sai dai maqabarta da ban-xaki” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Haka ma an hana sallah a makwantar Raquma, wato wurin da suke tattaruwa kuma suke kwana a wurin.

Sallah a maqabarta
Sallah a Ban-xaki
Sallah a makwantar Raquma

Abu Na Huxu : Suturce Al’aura

Al’aurar Namiji : ta fara ne daga cibiya zuwa gwiwa.

Al’aurar Mace a sallah : ita ce dukkan jikinta ban da fuskarta da tafukanta.

-Rufe Kafaxu Biyu :

Ya wajaba mai sallah ya rufe abinda yake tsakanin zira’insa da wuyansa, saboda faxin Manzon Allah (S.A.W) , “Kada xayanku ya yi sallah da tufa xaya, babu komai akan kafaxarsa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Abu Na Biyar : Fuskantar Alqibla

Alqibla dai ita ce Ka’abah mai girma.

Allah Mai girma da Buwaya ya ce, “Ka juyar da fuskarka inda masallaci mai alfarma yake, kuma a duk inda kuke ku juyar da fuskarku inda (masallaci mai alfarma) yake”. (Al-baqra : 144).

Ya wajaba a lura da abubuwa masu zuwa :

1 – Wajibi ne akan wanda yake sallah a cikin Masallacin Harami ya fuskanci ita Ka’abah kanta.

Amma wanda yake sallah a nesa da ita, to zai fuskanci inda take ne, saboda ba lallai ba ne ya iya fuskanta ita Ka’abar kanta ba, saboda Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Tsakanin inda rana take vullowa da inda take faxuwa alqibla take” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

2 – Sallar nafilar wanda yake kan abin hawa, alqiblarsa ita ce inda ya nufa, saboda abin da ya tabbata cewa Manzon Allah (S.A.W) “ya kasance yana yin nafila a kan abin hawansa, (yana kallon) duk inda ta yi da shi, yana yin wutiri a kanta, sai dai baya sallar farilla a kanta” [Abu Dawud ne ya rawaito shi]

Wanda yake sallah a nesa daga Ka’abah
Wanda yake yin salla a cikin Harami

-Wanda Bai San Inda Alqibla Take Ba, Yaya Zai Yi?

Wanda ba san inda alqibla take ba, in a ginannen wuri yake, ko akwai mutane a kusa da shi to sai ya tambaya, ko kuma ya gane alqiblar ta hanyar kallon wuraren liman a masallatai, ko kuma ya yi amfani da na’urar gano alqibla,

ko da rana ko wata da makamancin haka, idan ya kasa ganewa, sai ya yi gini a kan zato mafi rinjaye, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Ku ji tsoron Allah iya-iyawarku”. (At-tagabun : 16).Tags: