Sallolin Idi

13180

Alamun Idi

Idin musulmi guda biyu ne, idin buxa baki (Qaramar sallah), bayan watan Ramadan, da idin layya (Babbar sallah) bayan ranar Arafah.

Allah Maxaukakin Sarki ya canza mana da su daga idikan jahiliyya da ma duk wani idi qirqirarre.

An karvo daga Ansa xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, Mutanen jahiliyya suna da kwana biyu a shekara da suke wasa a cikinsu, yayin da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya zo Madinah, sai ya ce, “Kuna da kwana biyu da kuke wasa a cikinsu, kuma haqiqa Allah ya sauya musu da waxanda suka fi so alheri, idin buxa baki, da idin layya” [Nasa’i ne ya rawaito shi].

Baya halatta a yi tarayya da kafirai a cikin idinsu, saboda idi shi ne babbar alamar kowane addini ta fili, da tsarinsa.

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Kada ka bi son zuciyarsu wajen barin abin da ya zo maka na gaskiya, kowanne daga cikinku mun sanya masa shari’arsa da tsarinsa” (Al-ma’ida : 48).

Idi a musulunci ya haxa wasu ibadodi da bayyana farin ciki da cin abubuwa daxaxa na halal, saboda haka waxannan kwanaki suka zama kwanakin farin ciki da jin daxi, da ci da sha. Baya halatta a haxa idi da abin da ya sava wa koyarwar musulunci,

na cakuxuwar maza da mata, ko tozarta lokutan salloli, ko shan abin da aka haramta, ko wasa da abin da Allah ya haramta, ko jin abin da Allah ya haramta, ko wanin haka daga cikin abubuwan haramun.

Allah Maxaukakin Sarki ya shar’anta sallah a cikin idi biyu, sallar da take xaya daga cikin manya-manyan alamomin addini.

Hukuncin Sallar Idi Biyu

Farillah ce, da in wasu suka yi sun xauke wa sauran lafin rashin yin ta, duk da cewa umarni da ya zo da qarfi sosai, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi umarni da yin ta, kuma ya yi umarni a fito da mata, manya da qanana,

har ma da masu haila daga cikinsu, duk da baza su yi sallar ba, duk wannan don falalar sallar ne da qarfafa wa a kan yin ta. Dalilin kasancewarta farillah shi ne :

1- Faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Ka yi sallah ga Ubangijnka ka soke (Dabbarka)”(Al-kauthar : 2).

2- Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi umarni da ita, har da mata, saboda hadisin Ummu Axiyya – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi umarni da mu fitar da ‘yan mata, da masu haila, da ‘yan matan suke cikin xaki, zuwa sallar idin qaramar sallah da idin layya (Babbar sallah). Masu haila su nisanci wurin sallar, su halarci alheri da addu’ar musulmi” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Yadda Ake Sallar Idi Biyu

Sallar idi raka’a biyu ce, ba a kiran sallah, ba a yin iqama, ana bayyana karatu a cikinsu, ga yadda ake yin su :

1- Raka’ar farko zai yi kabbara bakwai, bayan ya yi kabbarar harama, ya yi addu’ar buxe sallah, kafin ya yi A’azu ya fara karatu.

2- Zai yi A’uzu ya yi bismillah, ya karanta fatiha da sura bayanta. Sunna ne ya karanta suratul ‹A’ala a raka’ar farko bayan ya yi fatiha, ya karanta suratul Gashiyah a raka’a ta biyu, ko kuma suratu Qaf a raka’ar farko, suratul Qamar a raka’a ta biyu.

3- Zai yi kabbara biyar a raka’a ta biyu, bayan kabbarar xagowa. Zai xaga hannayensa a kowace kabbara

4- Zai godewa Allah, ya yabe shi, ya yi salati ga Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) a tsakanin kabbarori

5- Idan ya yi sallama, sai ya hau minbari, ya yi huxuba biyu, ya zauna xan kaxan a tsakaninsu. Zai buxe huxubar farko da kabbarori tara, ta biyu da kabbara bakwai.

6- Mustahabbi ne a sallar qaramar sallah ya tunatar da mutane hukunce-hukuncen zakkar fidda kai, a babbar sallah kuma hukunce-hukuncen layya.

Wurin Da Ake Sallar Idi Biyu

A sunna dai shi ne a yi sallar idi a filin sallah ba a masallaci ba, in akwai buqata aka sallace ta a masallaci to babu laifi.

Abubuwan Da Ake So A Idi

1-Maza su yi ado da kyawawan kayansu, mata kuwa su fita sallah ba tare da ado da turare ba.

2-Mamu su sammakon zuwa, su shiga sahun farko

3-Ya tafi da wata hanya, ya dawo ta wata hanyar daban, a kan qafafunsa – in zai iya -. An karvo daga Jabir – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ya kasance ranar idi, yana canza hanya” [Bukhari ne ya rawaito shi]

4-Ya ci dabino uku ko biyar kafin ya fita sallar qaramar sallah. Amma a babbar sallah kada ya ci komai har sai ya dawo.

5-Ana son a xan jinkirta sallah idin qaramar sallah, saboda musulmi ya samu damar bayar da zakkar fidda kai, ta isa zuwa waxanda suka cancance ta. Amma babbar sallah ita ana so a yi ta da wuri.

Daga Hukunce-Hukuncen Idi

1- An karhanta sallar nafila kafin sallar idi da bayanta, sai dai in a masallaci za a yi ta, to sai a yi gaisuwar masallaci idan an shiga

2- Sunna ne idan sallar idi ta wuce, ko wani vangarenta ya kubce wa mutum, ya ramata kamar yadda take, ya sallace ta raka’a biyu da kabbarorinta, haka ma abin da ya rasa daga cikinta ya rama shi kamar yadda take.

3- Allah Maxaukakin Sarki ya shar’anta wa bayinsa a qarshen Ramadan su yi masa kabbara, Allah ya ce, “Don ku cika adadin kwanakin (Azumi) kuma don ku yi wa Allah kabbara a kan abin da ya shiryar da ku”. (Al-baqrah : 185).

Ma’anar ku yi wa Allah kabbara shi ne, ku girmama shi a cikin zukatanku da harsunanku.

Lafazin kabbarar shi ne : “Allahu Akbarul Lahu Akbar, La’ilaha Illal Lahu, Wal Lahu Akbar, Allahu Akbar, Walillahil Hamdu”.

4- Sunna ne maza su xaga muryarsu da waxannan kabbarori, mata kuwa za su voye, saboda an umarci mace ta sassauta muryarta.

5- Zai fara kabbarar idi tun daga faxuwar ranar daren idin, idan ya san da shigowar wata kafin faxuwar rana, kamar a ce mutane sun cika azumi kwana talatin, ko an ga jinjirin watan Shawwal.

Zai dakata da kabbara idan mutane sun fara sallar idi. Da babbar salla zai fara kabbara ne tun daga bayan sallar asubar ranar Arafa, zuwa sallar la’asar xin kwana ukun yanyane.

Faxakarwa

1- Ana son musulmi su yi wa junansu murnar idi.

2- Ana son bayyana farin ciki da idi, da yi wa ‹yan uwa da masoya da makusanta murna.

3- Idi wata dama ce da ya wajaba a ribace ta don sada zumuncin da aka yanke, da sulhunta wa tsakanin masu husuma.

4- Ba shar’anta ziyarar maqabarta ba a ranar idi, don hakan ya savawa farin cikin da annashuwar cikin idi.

5-An shar’anta yalwata wa iyali da tufafi da abinci da kayan cin daxi, waxanda Allah ya halatta, a ranar idi, saboda idi kwanaki ne na farin ciki da annashuwa.

Allah ya ce, “Ka ce da falalar Allah da rahamarsa ku yi farin ciki, shi ne ya fi alheri a kan abin da suke tarawa”. (Yunus : 58)

Taya Kafirai Murna A Ranar Idinsu
Baya halatta musulmi ya taya kafirai murnar idinsu, saboda a cikin haka akwai tabbatar da su a kan ayyukan kafirci da suke yi. Hakanan baya hallata zuwa inda suke idinsu da taya su farin ciki.


Tags: