Hukunce-Hukuncen Sallah

29235

1- Salla A Zaune

A – A Nafila :

Salla a zaune tana inganta a nafila, kuma yana da rabin ladan wanda ya yi a tsaye, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan ya yi sallah a tsaye wannan shi ya fi. Wanda kuwa ya yi sallah a zaune to yana da rabin ladan wanda ya yi a tsaye, wanda kuwa ya yi sallah a kwance to yana da rabin ladan wanda ya yi a zaune” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Idan kuwa ya yi sallah a zaune saboda uzuri to yana da lada cikakke, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan bawa ya yi rashin lafiya ko ya yi tafiya, za a rubuta masa (ladan) abin da yake aikata wa idan yana nan (bai yi tafiya ba) ko kuma idan yana da lafiya” [Bukhari ne ya rawaito shi].

B – A Farilla :

Sallah a zaune bata inganta a farillah in dai zai iya tsayuwa.

2- Niyya

Wasu Daga Hukunce-Hukuncen Niyya :

1 – Baya halatta a yanke niyya ana cikin sallah, wanda duk ya yi niyyar yanke sallah (wato fita daga sallah) to sallarsa ta vace, ya wajaba ya sake wata sabuwa.

2 – Wanda ya yi niyyar sallar nafila to baya halatta ya mayar da ita sallar farilla yana cikin sallar.

3 – Wanda ya yi niyyar sallar farilla shi kaxai, sai mutane suka zo masa, to ya halatta ya canza niyyarsa zuwa nafila, ya qarasa raka’a biyu, sannan sai ya yi sallama, ya yi sallah (Jam’i) tare da mutanen.

3- Karatun Fatiha

Wajibi ne akan mai sallah ya karanta fatiha, koda kuwa mamu ne, a cikin sallar da ake bayyana karatu. An karvo daga Ubada xan Samit – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun kasance a bayan Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) a cikin sallar asuba, sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi karatu, kuma karatun ya yi masa nauyi. Da ya gama sallar sai ya ce, “Wala’alla kuna karatu a bayan limaminku?” Sai muka ce “eh, haka ne ya Manzon Allah” Sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Kada ku sake aikata wa, sai dai fatiha, saboda babu sallah ga wanda bai karanta ta ba” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

4- Faxin "Ameen"

Sunna ne mai Sallah ya ce «Ameen», liman ne shi ko mamu, ko wanda yake sallah shi kaxai ne, sallar farilla ce ko nafila, a voye ake karatu ko a bayyane.

Ana voye faxin «Ameen» a sallar voye, ana bayyana shi a sallar bayyane.

Dalilin yin sa shi ne faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Idan liman ya ce “Ameen’’ kuma ku ce “Ameen”, saboda duk wanda amin xin shi ta dace da ta Mala’iku, an gafarta masa abin da ya gabata na Zunubansa” [Bukhari ne ya rawaito shi].

5- Wuraren Da Liman Yake Yin Shiru

1 – Yin shiru tsakanin kabbarar (harama) da karatun (fatiha) don yin addu’ar buxe sallah

2 – Yin shiru tsakanin fatiha da sura. Mamu zai karanta fatiha yayin da liman ya yi shirun

3 –Yin shiru bayan gama karatu kafin yin ruku’u

6- Bayyana Karatu A Sallar Nafila

Idan sallah ta wuce mutum, sai ya yi niyyar ramata, to zai voye karatu ne ko zai bayyana ne?

Sallar ake kallo ba lokacin ramata ba, da zai rama sallar da ake bayyana karatu da rana to zai bayyana karatu ne.

Abin da yake sunna shi ne voye karatu a sallolin nafiloli, sai dai wadda dalili ya zo da bayyana wa, kamar sallar asham, da kisfewar rana ko wata.

7- Xaga Hannaye

Ana xaga hannaye a wurare masu zuwa :

1 – Yayin kabbarar Harama

2 – Yayin kabbarar ruku’u

3 – Yayin xagowa daga ruku’u

4 – Yayin tashi daga tahiyar farko

8- Riskar Raka’ a

Idan mamu ya samu ruku’u da liman, to ya samu raka’a, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Duk wanda ya riski ruku’u to ya riski raka’a” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

9- Nutsuwa

Nutsuwa a cikin dukkan rukunan sallah rukuni ce, sallah bata inganta in babu ita, saboda abin da aka rawaito daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya shiga masallaci, sai wani mutum ya shigo ya yi sallah, sannan ya zo wajen Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi masa sallama, sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya amsa masa sallamarsa, sannan ya ce masa, “Koma ka yi sallah, don baka yi sallah ba”. Sai ya koma ya yi sallah kamar yadda ya yi a baya, sannan ya zo wajen Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi masa sallama, sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce “Walaikas Salam” sannan ya ce masa, “Koma ka yi salla, don kai baka yi sallah ba” Har ya yi haka sau uku. Sai mutumin ya ce wa Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Na rantse da wanda ya aiko ka da gaskiya ba zan iya wadda ta fi wannan kyau ba!, koya min” Sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Idan ka tashi yin sallah, ka yi kabbara, sannan ka karanta abin da ya sauwaqa gareka daga Alqur’ani, sannan ka yi ruku’u, har sai ka nutsu kana mai ruku’u, sannan ka xago, har sai ka daidaita kana tsaye, sannan ka yi sujjada har sai ka nutsu kana sujjada, sannan ka xago har sai ka nutsu kana zaune. Ka aikata haka a dukkan sallarka gaba xaya” [Bukhari ne ya rawaito shi].

10- Motsa Harshe

Karatun zuci baya wadatar wa a wajen karatun Alqur’ani da kabbarori da zikirai, dole sai an yi furuci da abin, mafi qaranci a motsa harshe da lavva yayin karatun.

11- Yadda ake sujjada

Sunna ita ce nuni da xan yatsa a tahiya, saboda hadisin Wa’il xan Hujr – Allah ya yarda da shi – “Sannan ya xaga xan yatsansa, sai na ganshi yana motsa xan yatsan, yana addu’a da shi” [Nasa’i ne ya rawaito shi].

12- Nuni Da Xan Yatsa

Ana yin sujjada akan gavvai bakwai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ”Idan bawa ya yi sujjada, sai gavvai bakwai su yi sujjada tare da shi, fuskarsa, da tafukansa biyu, da gwiwowinsa biyu, da qafafuwansa biyu” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].Tags: