Siffar Yadda Ake Sallah

66442

Fuskantar Alqibla Da Kabbarar Harama

1- Wanda zai yi sallah zai tsaya, yana mai fuskantar alqibla, yana mai jin tsayuwarsa gaban Allah Maxaukakin Sarki, mai qasqantar da kansa a cikin sallarsa.

2- Sannan sai ya yi niyyar sallah a cikin zuciyarsa.

3- Sai ya xaga hannayensa daidai kafaxunsa ko kunnuwansa, ya ce “Allahu Akbar” [Muslim ne ya rawaito shi].

4- Sannan sai ya sanya hannunsa na dama akan na hagu a kan qirjinsa [Ahmad ne ya rawaito shi], ko kuma ya riqe hannun hagu da damansa.

Buxe Sallah Da Karatun Fatiha

- Mai sallah zai sunkuyar da kansa, ya sanya ganinsa zuwa inda zai yi sujjada [Bukhari ne ya rawaito shi], sannan ya ce, “Subhanakal Lahumma Wabi Hamdika, Tabarakas Muka, Wata’ala Jadduka, Wala’ilaha Gairaka” [Muslim ne ya rawaito shi].

- Sannan bayan haka sai ya ce, “A’uzu Billahi Minash Shaixanir Rajim, Bismillahir Rahmanir Rahim” [Muslim ne ya rawaito shi].

- Bayan haka sai ya karanta fatiha [Bukhari ne ya rawaito shi] , ya ce, “Amen” (A Qarshen ta) Ma’ana Allah ka amsa.

- Sannan sai mai sallah ya karanta fatiha da sura, ko kuma abin da ya sauwaqa daga Alqur’ani a raka’a biyun farko, ya bayyana karatu a sallar asuba, da raka’o’in biyun farko a sallar magariba da isha.

Xagowa Daga Ruku’u

- Mai sallah zai xaga hannayensa, yana mai kabbara, ya tafi ruku’u, ya sanya hannayensa akan gwiwowinsa, yana mai buxe ‹yan yatsunsa, yana mai damqar gwiwowinsa, ya daidaita bayansa da kansa, sannan ya ce, “Subhana Rabbiyal Azim” [Tirmizi ne ya rawaito shi] sau uku.

- Sannan sai ya xago ya ce, (Liman ne ko wanda yake yi shi kaxai) “Sami’allahu Liman Hamidahu”[Tirmizi ne ya rawaito shi]

ya ce, (kowa da kowa) : “Rabbana Walakal Hamdu, Mil’as Samawati, Wa Mil al’ard, Wa Mil’a Ma Baina huma, Wa Mil’a Ma Shi’ata Min Shai’in Ba’adu” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

An so ya xora hannayensa akan qirjinsa, kamar yadda ya yi kafin ya yi ruku’u.

Sujjada Da Xagowa Daga Gareta

Mai sallah zai yi kabbara, sannan ya tafi zuwa sujjada, ya zama farkon abin da zai fara sauka a kan qasa gwiwowinsa, sannan hannayensa, sai goshinsa da hancinsa, ya shimfixa tafukansa akan qasa, (ya sanya su) daidai da kunnuwansa ko kafaxunsa.

Ya sanya ‹yan ‹yatsun hannayensa su kalli alqibla, ya xaga tsintsiyar hannunsa daga qasa, ya nisantar da dantsensa daga geffensa, cikinsa kuma daga cinyoyinsa, ya ce, «Subhana Rabbiyal A’ala” sau uku, ya yawaita addu’a a cikin sujjadarsa [Muslim ne ya rawaito shi].

-Sannan ya xago kansa yana mai kabbara [Muslim ne ya rawaito shi], kada ya xaga hannayensa, ya zauna yana mai shimfixa qafarsa ta hagu, ya kafe ta dama, ya sanya ‹yan ‹yatsun qafafun nasa su kalli alqibla, ya ce, “Allahummag firli, War’amni, Wajburni, Wahdini, Warzuqni” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

-Sannan ya yi kabbara, ya yi sujjada ta biyu kamar yadda ya yi ta farko.

-Sannan sai ya xago kansa yana mai kabbara, ya zauna xan kaxan, zaman da ake kiransa da “Jilsatul Istiraha” Saboda hadisin Malik xan Huwairis – Allah ya yarda da shi – a wajen siffata sallar Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) cewa shi Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Bai miqe ba (daga sujjada) har sai da ya daidaita a zaune” [Bukhari ne ya rawaito shi].

-Sannan sai ya tashi zuwa raka’a ta biyu yana mai kabbara, mai dogaro akan hannayensa [Bukhari ne ya rawaito shi].

-Ya sallaci raka’a ta biyu kamar yadda ya yi ta farko, sai dai ba zai faxi addu’ar buxe sallah ba.

Tahiya

- Idan mai sallah ya gama raka’o’in biyun farko sai ya zauna don yin tahiyar farko, yana mai shimfixa qafarsa da hagu, ya kafe ta dama, ya sanya hannayensa akan cinyoyinsa, ya shimfixa hannunsa na hagu, ya kame xan qaramin ‹yatsansa da mai bi masa da na tsakiya, ya xaga xan ‹yatsansa manuniya, ya yi nuni da shi yayin tahiya, ya riqa kallonsa ya ce, “Attahiyyatu Lillahi, Wassalawatu, Waxxayyibatu, Assalamu Alaika Ayyuhan Nabiyyu, Warahmatullahi Wabarakatuhu, Assalamu Alaina Wa’ala Ibadullahis Salihina, Asshahadu An la’ilaha Illah Lahu, Wa Asshahadu Anna Muhammadan Abduhu Warasuluhu” [Bukhari ne ya rawaito shi].

- Sannan ya miqe yana mai kabbara, ya xaga hannayensa yayin kabbarar, ba zai karanta komai ba a sauran raka’o’in sai fatiha kaxai.

- Ya zauna a harxe a tahiyar qarshe, Ma’ana ya zuro qafarsa ta hagu daga bangaren damansa yana mai shimfixata, ya zauna akan mazaunarsa, qafarsa ta dama kuma ya kafe ta, ya faxi abin ya zo a tahiya ta farko, ya qara a kai da cewa : “Allahumma Salli Ala Muhammad, Wa’ala Aali Muhammad, kama Sallaita Ala Ibrahim, Wa ala Aali Ibrahim, Innaka Hamidun Majid. Allahumma Barik Ala Muhammad, Wa’ala Aaali Muhammad, Kama Barakta Ala Ibrahim, Wa’ala Aali Ibrahim, Innaka Hamidun Majid” [Bukhari ne ya rawaito shi].

- Sannan ya ce, “Allahumma Inni A’azu Bika Min Azabi Jahannama, Wamin Azabil Qabri, Wa min Fitnatil Mahya Wal Mamati, Wa min Sharri fitnatil Masihil Dajjal” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Sallama

A qarshe, mai sallah zai yi sallama a vangaren damansa ya ce, “Assalamu Alaikum” [Muslim ne ya rawaito shi] a hagun sa ma hakan.

Kabbara
Xora Hannu Akan Qirji
Ruku’u
Sujjada
Zama Tsakanin Sujjadu Biyu
Zaman Tahiya
Sallama

Daga Cikin Zikiran Da Ake Yi Bayan Sallah

-“Astagfirullahi” sau uku, “Allahumma Antas Salam, Wa minkas Salam, Tabarakta Yaa Zal Jalal Wal Ikram” [Muslim ne ya rawaito shi].

-“Laa ilaha Ilal Lahu, Wahdahu La sharika Lahu, Lahul Mulku, Walahul Hamdu, Wa huwa Ala kulli Shai’in Qadiir. Allahumma La mani’a lima aaxaita, Wala mu’uxiya lima Aaxait, Wala Yanfa’u Zal Jaddi Minkal Jadd” [Bukhari ne ya rawaito shi].

-“Laa ilaha Ilal Lahu, Wahdahu La sharika Lahu, Lahul Mulku, Walahul Hamdu, Wa huwa Ala kulli Shai’in Qadiir. La haula wala quwwata illa billahi, Laa ilaha illal Lahu, Wala Na’abudu Illa Iyyahu, Lahun ni’imatu Walahul Fadlu, Walahus sana’ul Hasan, Laa ilaha Ilal Lahu, Mukhlisina lahudden, Walau karihal Kafiruun” [Muslim ne ya rawaito shi].

-“Subhanallah, Wal Hamdu Lillahi, Wallahu Akbar” Sau talatin da uku. “Laa ilaha Ilal Lahu, Wahdahu La sharika Lahu, Lahul Mulku, Walahul Hamdu, Wa huwa Ala kulli Shai’in Qadiir” [Muslim ne ya rawaito shi].

-“Allahumma A’inni Ala Zikrika, Wa shukrika, Wa Husni Ibadatika” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

- Karanta ayatul Kursiyyi, da suratul Al-ikhlas, da Falaqi da Nasi [Nasa’i ne ya rawaito shi].

- Faxin “Allahumma Inni As’aluka Ilman Nafi’an, Wa zirqan Xayyiban, Wa amalan Mutaqabbalan” [Ibnu Majah ne ya rawaito shi] Bayan an yi sallah daga sallar asuba.

An karvo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana buxe sallah da kabbara, karatu kuma da “Alhamdu Lillahi Rabbil Aalamin”. Hakanan ya kasance idan ya yi ruku’u baya xaga kansa sama, kuma baya sunkuyar da shi qasa, sai dai yana sanya shi tsakanin haka. Idan ya xago kansa daga ruku’u baya sujjada har sai ya daidaita a tsaye, hakanan idan ya xago daga sujjada baya komawa sujjada har sai ya daidaita a zaune. Ya kasance yana faxin tahiya a dukkan tsakanin raka’o’i biyu. Hakanan ya kasance yana shimfixa kafarsa ta hagu, ya kafe ta dama (a zaman tahiya). Ya kasance ya hana zaman shaixan (zama akan dugadugai), yana hana mutum ya shimfixa tsintsiyar hannunsa kamar yadda dabbobi suke yi. Yana qare sallah da sallama” [Muslim ne ya rawaito shi].

Mas’aloli :

1-Wasu mutanen suna jin zafi da raxaxi idan suka yi zaman da ake so a tahiya da tsakanin sujjadu guda biyu, to irin waxannan babu laifi a kansu su zauna zaman da za su iya, saboda wahala da tsanani suna kawo rangwame a shari’ar musulunci.

2-Mace daidai take da namiji a wajen yadda ake yin sallah, komai-da-komai.Tags: