Sujjadar Godiya

11909

Na Farko : Sujjadar Rafkanuwa

Bayanin Sujjadar Rafkanuwa

Sujjadar Rafkanuwa ita ce,

Sujjadu guda biyu da mai sallah yake yin su, saboda gyara wani tasgaro da ya faru saboda mantuwa a cikin sallah

Sababan Yin Sujjadar Rafkanuwa

Sababan Sujjadar Rafkanuwa guda uku ne, Shakka, qari, ragi

1- Shakka ita ce,

Shakka ita ce,

Kai-kawo tsakanin abubuwa biyu, kan wanne ne ya faru

Shakka a sallah ta kasu kaso biyu :

1- Shakka Bayan Sallah

- Irin wannan shakkar ba a kallonta

Misali : Mutum ne ya yi shakka bayan sallar asuba cewa shin ya yi ta raka’a biyu ne ko uku? To irin wannan shakkar ba a kallonta sai dai in an tabbatar, sai a yi aiki da abin da aka tabbatar.

2- Shakka a cikin Sallah

Irin wannan shakkar bata wuce xayan biyu :

A – Xayan abubuwa biyun ya rinjaya a gare shi

To anan zai yi aiki da abin da ya rinjaya a gare shi, ya yi sujjadar rafakanuwa bayan sallama.

Misali : Mutum ne yana sallar azzahar, sai ya yi shakka, shin a raka’a ta biyu yake ko ta uku, amma ya rinjaya a gare shi cewa ta uku ce, to sai ya sanyata ta uku, ya cika sallarsa, sannan sai ya yi sujjadar rafkanuwa bayan sallama.

Dalili akan haka, faxin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan xayanku yayi shakka a sallarsa, to ya kintaci daidai, sannan ya yi sallama, sannan kuma ya yi sujjadar rafkanuwa guda biyu” [Ibnu Hibban ne ya rawaito shi]

Yana Sallama sannan Yana Sujjadar Rafkanuwa

B – Ya zama babu wani abin da ya rinjaya a gare shi a cikin abubuwan guda biyu :

To anan sai ya yi gini akan mafi qaranci, ya cika sallarsa, ya yi sujjadar rafkanuwa kafin sallama.

Misalinsa : Mutum ne ya yi sallar azzahar sai ya yi shakka shin a raka’a ta biyu yake ko ta uku, amma ba abin da ya rinjaya a gare shi, to sai ya yi gini akan mafi qaranci, ya xauke ta raka’a ta biyu, ya cika sallarsa, ya yi sujjadar rafkanuwa kafin sallama.

Dalili akan haka shi ne faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Idan xayanku ya yi shakka a cikin sallarsa, bai san nawa ya sallata ba, uku ne ko huxu, to ya jefar da shakkar, ya yi gini akan abin da ya tabbatar, sannan ya yi sujjadu guda biyu kafin ya yi sallama” [Muslim ne ya rawaito shi]

Yana Sujjadar Rafkanuwa Sannan Yana Sallama

2- Qari

Shi ne mai sallah ya yi qari a cikin sallarsa, ya qara ruku’u ko sujjada.

Kuma qari baya wuce hali biyu :

A – Mai sallah ya tuna da qarin yana cikin sallah

Anan wajibi ne ya bar wannan qarin, ya cika sallarsa, sannan ya yi sujjadar rafkanuwa bayan sallama.

Misalinsa : Mutum ne yana sallar azzahar, sai ya tashi zai kawo raka’a ta biyar, sai ya tuna yana cikin raka’ar, to anan wajibi ne a kansa ya zauna da gaggawa, ya cika sallarsa, sannan ya yi sujjadar rafkanuwa guda biyu bayan sallama.

B – Mai sallah ya tuna qarin bayan ya yi shi.

To anan zai cika sallarsa, sannan ya yi sujjada bayan sallama.

Dalilin haka hadisin Abdullahi xan Mas’ud – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi sallar azzahar raka’a biyar, sai aka ce masa, “An qara sallah ne?” sai ya ce, “Me ya faru?” sai ya ce, “Ka yi sallah raka’a biyar” sai ya yi sujjada biyu bayan ya yi sallama”[Bukhari ne ya rawaito shi].

3- Ragi

Shi ne Mai sallah ya rage rukini ko wajibi daga cikin rukunai ko wajiban sallah .

1 – Rage Rukuni

Idan wannan rukunin da ya rage kabbarar harama ce to sallah ta vace, saboda tun asali ma bata qullu ba, idan rukunin ba kabbarar harama ba ne, to xayan biyu :

A – Mai sallah ya tuna bayan ya kai wajen irin wannan rukunin a raka’a ta gaba

To anan zai jefar da wannan raka’ar wandda ya bar rukuni a cikinta, ya mayar da wadda take binta a matsayinta.

Misalinsa : Mutum ne ya manta ruku’u a raka’ar farko, sai ya tuna a lokacin da yake cikin ruku’un raka’a ta biyu, cewa ya manta da ruku’u a raka’ar farko, to sai ya xauki wannan raka’a ita ce raka’ar farko, ba zai yi lissafi da raka’ar da ta gabata ba, sai ya cika sallarsa, sannan ya yi sujjadar rafkanuwa bayan sallama.

Ya yi sallama Sannan Yana sujjadar rafkanuwa

B – Mai Sallah ya tuna kafin ya kai wurin irin wannan rukuni da raka’a ta gaba.

To anan sai ya koma ya zo da waccan rukuni da ya bari da abin da yake bayansa, sai ya cika sallarsa, sannan ya yi sujjadar rafkanuwa bayan sallama.

Misalinsa : Mutum ne ya manta sujjada ta biyu da zama kafinta na raka’ar farko, bayan ya tashi daga ruku’u na raka’a ta biyu sai ya tuna cewa bai yi sujjada ta biyu ba da zamanta a raka’a ta farko, to sai ya koma ya zauna ya yi sujjadar, sannan ya cika sallarsa, ya yi sujjadar rafkanuwa bayan sallama.

2 – Rage Wajibi

Idan mai sallah ya manta wajibi daga cikin wajiban sallah, to baya fita daga xayan halin uku :

A – Ya tuna shi kafin ya bar mahallinsa a cikin sallah

To anan zai zo da shi, kuma babu komai a kansa

B – Ya tuna shi bayan ya bar wurin da ake wajibin a cikin sallah, amma kafin ya kai rukunin da yake bin sa.

To anan zai koma ya zo da shi, sannan ya cika sallarsa, ya yi sujjadar rafkanuwa bayan sallama.

C – Ya tuna wajibin bayan ya shiga cikin rukunin da yake bin sa.

To anan zai ci gaba da sallarsa, ba zai dawo baya ba, sai ya yi sujjada bayan sallama.

Misalinsa : Mutum ne ya xago daga sujjada ta biyu ta raka’a ta biyu, sai ya tashi zuwa raka’a ta uku, ya manta da zaman tahiyar farko, amma sai ya tuna ya manta da tahiyar farko tun kafin ya miqe, to zai koma ya zauna ya yi tahiya, sannan ya cika sallarsa, babu komai a kansa.

Idan ko ya tuna bayan ya tashi amma kafin ya tabbata a tsaye, sai ya dawo ya zauna ya yi tahiya, sannan sai ya cika sallarsa ya yi sujjadar rafkanuwa kafin sallama.

Idan kuwa ya tuna bayan ya tashi ya miqe qam, to tahiyar ta faxi daga kansa, ba zai koma ba, zai cika sallarsa, ya yi sujjadar rafkanuwa kafin sallama.

Dalili akan haka hadisin Abdullahi xan Buhaina – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi mana sallar azzahar, sai ya miqe a raka’a ta biyun farko bai zauna ba, sai mutane suka miqe tare da shi, har sai da ya gama sallah, mutane suna jiran ya yi sallama, sai ya yi kabbara yana zaune, ya sujjadu biyu kafin ya yi sallama, sannan ya yi sallama.” [Bukhari ne ya rawaito shi]

Daga abin da ya gabata zamu gane cewa sujjadar rafkanuwa tana kansancewa kafin sallama da bayan sallama.

Siffar Sujjadar Rafkanuwa

Mai sallah zai yi kabbara, sannan sai ya yi sujjadu guda biyu, kamar yadda ake sujjada a cikin sallah, sannan sai ya yi sallama bayan ya yi su.

Mas’aloli :

1 – Idan mai sallah ya yi sallama kafin sallarsa ta cika, bai tuna ba sai bayan lokaci mai tsawo, to zai sake sabuwar sallah.

Idan kuwa ya tuna bayan xan lokaci kaxan kamar minti biyu ko uku, to sai ya dawo ya cika sallarsa, ya yi sujjadar rafkanuwa bayan gama sallar.

2 – Wajibi ne akan mamu ya bi liman a cikin sujjadar rafkanuwa koda kuwa ya samu liman xin ne bayan ya yi rafkanuwar.

3 – Idan rafkanuwa biyu ta haxu ga mai sallah, xaya ana yin ta ne bayan kafin sallama, xaya kuma bayan sallama, to shi zai yi sujjadar rafkanuwa ne sau xaya kafin sallama.

Abu Na Biyu : Sujjadar Godiya.

Sujjadar Godiya

Ita ce yin sujjada don godewa Allah yayin samuwar wata ni’ima, ko wani lamari mai daxi, ko kuma kuvuta daga wani mummunan abu, da makamancin haka.

Dalilin Sujjadar Godiya hadisin Abi Bakrata – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance idan wani abu na farin ciki ya zo masa, ko aka yi masa bushara da shi, sai ya faxi ya yi sujjada, don godiya ga Allah” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Siffar Sujjadar Godiya

Zai yi kabbara yana mai sujjada, ya ce, "Subhanal Rabbiyar A’ala" ya gode wa Allah akan ni’imar da ya yi masa, sannan ya xago daga sujjadarsa, ba zai kabbara ba ko sallama.

Abu Na Uku : Sujjadar Tilawa

Sujjadar tilawa

Iita ce sujjadar da mai karatu yake yi idan ya karanta ayar da take akwai sujjada a cikinta

Dalilin sujjadar tilawa shi ne abin ya tabbata daga Abdullahi xan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana karanta mana surar da take akwai sujjada a cikinta, sai ya yi sujjada, muma sai mu yi sajjada” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Ana yin wannan sujjada idan mai karatu ya wuce ta kan ayar da take akwai sujjada a cikinta, koda kuwa yana cikin sallah ne, kuma koda a voye yake karatu ko a sarari. Hakama idan ba a sallah yake ba. Babu sharaxin sai yana da alwala

Siffar Sujjadar Tilawa

- Mai karatu ko wanda yake saurare zai yi kabbara don yin sujjadar, ya kuma ce, “Subhanal Rabbiyar A’ala” ya yi addu’a ya ce, “Sajada Wajhi Lillazi Khalaqahu, Wa Shaqqa Sam’ahu Wa Basarahu, Bi haulihi Wa quwwatihi” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

- “Allahummak Tub Li Biha Indika Ajran, Wa da’a anni biha wizra, waj’alha li indaka zukhra, wata qabbalha minni kama taqabbaltaha min abduka Dawud” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Sannan sai ya yi kabbara ya xago daga sujjada, in a sallah ne, in kuma ba a sallah ba ne ba, sai ya xago ba tare da kabbara ko sallama ba.

Ayoyin Da suka Qunshi Sujjadar Tilawa : sune

Suratu Al-a’araf aya ta (206)
Suratur Ra’ad aya ta (15)
Suratun Nahli aya ta (49)
Suratul Isra’I aya ta (107)
Suratu Maryama, aya ta (58)
Suratul Hajj, aya ta (18)
da aya ta (77)
Suratul Furqan, aya ta (60)
Suratun Namli, aya ta (25)
Suratus Sajda, aya ta (15)
Suratu Saad, aya ta (24)
Suratu Fussilat, aya ta (37)
Suratun Najmi, aya ta (62)
Suratul Inshiqaq, aya ta (21)
Suratul Alaq, aya ta (19)

Mas’aloli :

1 – Matafiyi akan abin hawa idan ya karanta ayar da take da sujjada, sai ya sauka daga kan abin hawan nasa ya yi sujjadar tilawa, idan kuwa hakan bai samu ba to sai ya yi nuni da kansa zuwa sujjada.

2 – Idan mai karatu ya maimata ayar sujjada to zai yi sujjada xaya ce kawai.

3 – Babu laifi a wajen yin sujjadar tilawa a lokatan da aka hana sallah a cikinsu.

4 –Idan mai karatu bai yi sujjada ba, to mai sauraro shi ma ba zai yi ba, saboda yana koyi ne da mai karatu.

5 – Wanda yake jin karatu ba tare da ya yi niyyar saurare ba, kamar ya zama wucewa yake, ko kuma ya shagalta da wani abu, to ba zai yi koyi da mai karatu ba wajen sujjadar tilawa, don bai bi shi a karatun ba.



Tags: