Daga Ladubban Sallah

5630

Sallah ibada ce mai girma, musulmi yana fuskantar Allah da zuciyarsa da jikinsa a cikinta, saboda haka ya kamata kafin a yi ta, a yi shiri na zuciya da jiki, don samun damar yin ta, da bayar da ita fuskar da ta dace, saboda haka aka shar’anta abubuwan da za su zo :

1 – Tsarkake Zuciya

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ba a umarce su da komai ba, face su bautawa Allah suna masu tsakake addini gare shi, suna karkata zuwa ga gaskiya, su tsaida sallah, su bada zakkah, wannan shi ne addini miqaqqe”. (Al-bayyina : 5).

Allah baya karvar aiki sai in ya kasance tsarkakke don Allah, babu riya ko jiyar wa, ko wani abu daga cikin abubuwan da suke shirka ne ga Allah.

2 – Kyautata alwala

Shi ne kyautata yin ta, akan cikarkiyar kama.

An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Ba zan nuna muku abin da Allah yake goge zunubi da shi ba, kuma yake xaga daraja da shi ba?” sai suka ce, “Nuna mana ya Manzon Allah” Sai Manzon Allah ya ce, “Kyautata alwala a lokacin da ake qi (kamar lokacin sanyi) [Lokacin da ba a so shi ne lokacin da alwala take yi wa mutum wahala, saboda sanyi da makamancinsa], da yawan taku zuwa masallaci, da jiran salla bayan an yi wata sallar, wannan kuwa shi ne ribaxo” [Muslim ne ya rawaito shi].

3 – Gaggawar Zuwa Sallah

Shi ne fita da wurwuri, saboda a samu falalar jiran sallah. An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Xayanku ba zai gushe ba yana cikin sallah, matuqar dai sallah yake jira” [Bukhari ne ya rawaito shi].

4 – Ambaton Allah

- Ya ambaci Allah yayin da zai fita daga gida, ya ce, “Bis Millahi, Tawakkaltu Alal Lahi, Wala Haula Wala Quwwata Illah Billahi”. Ma’ana : (Da sunan Allah, na dogara ga Allah, babu wata dabara ko qarfi sai ga Allah”. Sannan ya ce, “Allahumma Inni A’uzu bika an adillah au Udallah, au azillah au uzallah, au azlima au uzlama, an ajhala au yujhala alayya” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

-“Ma’ana : Ya Allah ina neman tsarinka kada in vace ko a vatar da ni, ko in kauce ko a kautar da ni, ko inyi zalunci ko a zalunce ni, ko in yi wauta ko a yi min wauta” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

- Ya ambaci Allah yayin tafiya masallaci ya ce, “Allahummaj al fi qalbi nuran, wafi lisani nura, waj al fi sam’i nura, waj al fi basari nura, waj al min khalfi nura, wa min amami nura, waj al fi fauqi nura, wa min tahti nura, Allahumma a’axini nura”.“ma’ana : Ya Allah ka sanya haske a cikin zuciyata, ka sanya haske a cikin harshena, ka sanya haske a cikin ji na, ka sanya haske a cikin ganina, ka sanya haske a bayana, da gabana, ka sanya haske a samana da qarqashi na, Ya Allah ka bani haske” [Muslim ne ya rawaito shi].

5 – Tafiya zuwa masallaci a hankali da nutsuwa

Saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Idan kun ji iqama ta fi zuwa ga sallah, kuna cikin nutsuwa da hankali, kada ku yi gaggawa, abin da kuka samu ku sallata, abin da ya wuce ku, ku ciko” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

6 – Zikiri Yayin Shiga Da Fita Daga Masallaci

-Yayin shiga masallaci zai ce, “A’uzu Billahil Azim, Wabi wajhihil Karim, Wa sulxanihil Qadim, minash Shaixanil Rajim” “Bis millahi, Wassalatu Wassalamu Ala Rasulullahi” Allahumma iftah li abwaba Rahmatika” (Ma’ana : Ina neman tsari daga wajen Allah mai girma, da fuskarsa mai girma, da ikonsa daxaxxe, daga shaixan jefaffe”. “Da sunan Allah, Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah” “Ya Allah ka buxe min qofofin rahamarka” [Muslim ne ya rawaito shi].

-Yayin da zai fito daga masallaci sai ya ce, “Bismillahi, Wassalatu Wassalamu Ala Rasulillahi, Allahumma inni As’aluka min Fadlika, Allahumma’ asimni minash Shaixanir Rajim”. (Ma’ana : Da sunan Allah, tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah. Ya Allah ina roqonka daga falalarka, ka tsare ni daga Shaixan jefaffe” [Ibnu Majah ne ya rawaito shi].

7 – Kada Ya Zauna Har Sai Ya Yi Nafila Raka’a Biyu

Saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan xayanku ya shiga masallaci, to ya yi raka’a biyu kafin ya zauna” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

8 – Nisantar sarqafe ‘yan yatsun hannu

Saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) , “Idan xayanku ya yi alwala, ya kyautata alwalarsa, sannan ya fita ya nufi masallaci, to kada ya sarqafe ‘yan ‘yatsunsa, saboda shi yana cikin sallah ne” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

9 – Shagalta Da Zikiri :

Kujishughulisha kumtaja Mwenyezi Mungu, kuobma dua na kusoma Qur’ani wakati wa kungojea Swala bila kuwafanyia fujo wenye kuswali.

10 – Qanqantar Da Kai Da Tsoron Allah A Cikin

Wannan shi ne tushen sallah da ranta, saboda sallar da ba qasqantar da kai da tsoron Allah da halarto da zuciya a cikinta, kamar jiki ne matacce babu rai.

Ibnu Rajab – Allah ya ji qansa – ya ce, “Asalin Qasqantar da kai da nutsuwa shi ne, zuciya ta yi taushi, ta samu nutsuwa da qasqanta da karye wa da qone wa, idan zuciya ta nutsu to duk sauran gavovi ma sai su samu nutsuwa, saboda dukkansu suna bin zuciya ne” [Duba littafin “Alkhushu’u” Na Ibnu Rajab].

Mahallin nutsuwa da tsoron Allah shi ne zuciya, gavovi kuwa shi ne suka faxin abin da yake cikin zuciya..Basi unyenyekevu mahali pake ni moyo, na ulimi wake wenye kueleza ni viungo.

11 – Lazimtar Sunnar Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) A Cikin Sallarsa Gabaxaya.

Sallah ibada ce da ya wajaba a bi Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) a cikinta, kada mai sallah ya aikata wani abu ko ya faxi wani abu wanda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) bai aikata shi ba, ko bai faxe shi ba, saboda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Ku yi sallah kamar yadda kuka ga ina yi” [Bukhari ne ya rawaito shi].



Tags: