Abubuwan da suka halatta a cikin Sallah

2640

ABUBUWAN DA DARASIN YA KUNSA
1- Abubuwan da suka halatta a cikin Sallah
2- Abubuwan da suke makaruhai a cikin Sallah
3- Abubuwan da suke'bata Sallah

NA FARKO : ABUBUWAN DA SUKA HALATTA A CIKIN SALLAH

1- Tafiya a cikin Sallah saboda wata illa da ta faru, sharadin rashin kaucewa alkiblah, kamar buɗe wata kofa da take bangaren alkiblah
2- Ɗaukar yara a cikin Sallah
3- Kashe macijiya da kunama a cikin Sallah
4- Wai-waye a cikin Sallah saboda wata buƙata
5- Yin kuka a cikin Sallah
6- Cewa Subhanallah ga maza, da yin tafi ga mata idan an samu rafkanuwa
7- Yin Tuni ga Limami idan ya bata a karatun Sallah
8- Yin nuni a cikin Sallah dan maida sallama da ɗan yatsa ko hannu ( Sai Ya Sanya Tafin Hannun Sa Akan Ƙasa Bayan Hannun A Sama )
9- Nuni wanda zai nusantar da mai Sallah saboda wata buƙata da ta bujuro
10- Godewa Allah Madaukakin sarki idan ya ga abinda ya roƙye shi
11- Yin Tofi da Kaki a cikin Sallah bangaren hagu
12- Hana wucewa ta gaban mai Sallah

NA BIYU : ABUBUWAN DA SUKE MAKARUHAI A CIKIN SALLAH

1- Shigar mutum masallaci yana mai sanya tunani ko wajan sa ko a gaban sa akwai a binda zai ɗauke masa hankali gama da Sallah: Kamar Matsuwar Fitsari, ko Kashi ( bayan gari / bayan gida ) ko Tusa ( huto ), ko Yunwa ko Ƙishirwa, ko a kawo wani abinci da zai ɗauke masa hankali, ko Yayi ta kallon wani abu da zai kawar da shi daga Sallah.
2- Wasa, Shi ne aikin da zai ko rewa mutum kushu'i da Nutsuwa a cikin Sallah
Misali: Motsi ba tare da wata buƙata ba, da wasa da gemu, da tufafi, da rawani ( wato abinda larabawa suke ɗora shi akan hirami ), da agogo, da lanlan-kwasa yan yatsu, da dunkule su, da makamantan haka.
3- Juyar da fuska a cikin Sallah, ba tare da buƙata ba, da sharadin rashin juyawar jiki ga barin alkiblah, idan ba haka ba Sallah ta ɓaci.
4- Riƙe ƙugu : Shi ne mutum ya sanya hannun sa a kan ƙugu, saboda yin hakan yana daga cikin aikin Yahudawa.
5- Lullube ba'ki da hanci a cikin Sallah.
6- Shimfida tufafi da hannun riga a cikin Sallah.
7- Kame gashi da tattara shi da tifke shi ga maza, sai ya zamo kaman-cece-niya da Maktu'uf ; wanda ya daure hannunsa a bayan sa, idan zai yi sujjada gashin shi baya sujjada tare da shi.
8- Tofi bangaren alkiblah ko damar mai Sallah.
9- Kallon Sama.
10- Rumtse idanuwa, sai da buƙatar hakan.
11- Shimfida zura'i a cikin sujjada.

ABUBUWAN DA SUKE 'BATA SALLAH

1- Zuwa da abinda yake kore sharadi daga cikin sharuddan, kamar isuwa ga abinda yake bata Sallah, ko yaye tsaraici da gangan, ko karkace wa alkiblah da dukkan jikin sa, ko yanke-war niyya.
2- Barin wani rukuni da gangan ko wajibi a cikin Sallah.
3- Yawaita ayyuka masu yawa a cikin Sallah, idan suka zamo basa daga cikin jinsin Sallah, kuma ya kasance ba da larura ba, kamar tafiya da yawan motsi.
4- Dariya da ƙyaƙyata dariya.
5- Magana da gangan.
6- Ci da Sha da gangan.
7- Ƙara wata raka'a ko rukuni da gangan.
8- Sallamar ma-mu da gangan kafin limamin sa.


Tags: