Taimama

20364

Bayanin Mece Ce Taimama

Ma’anar Kalmar "Taimama" a larabce

Shi ne nufin wani abu da fuskantarsa

Ma’anar taimama a shari’a

Ita ce, shafar fuska da hannaye biyu da qasa mai tsarki, da niyyar xahara.

Hukuncin Taimama

Taimama tana wajaba idan aka rasa ruwa, ko kuma a kasa amfani da shi, don yin wani abin da tsarki ya wajaba a cikinsa kamar sallah, tana zama mustahabbi cikin abin da tsarki yake mustahabbi a cikinsa kamar karatun Alqur’ani

Dalilan Yin Taimama

1 - Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ba ku samu ruwa ba, to ku yi taimama a wuri mai tsarki, ku shafi fuskokinku da hannayenku daga gare shi”. (Alma’ida : 6).

2 - Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “An ba ni abubuwa biyar, waxanda ba a baiwa wani Annabi ba gabani na ba, an taimake ni da sanya tsoro cikin zukatan maqiya tsawon tafiyar wata guda, an sanya min qasa ta zamar min wurin sallah da tsarki, ko wanene daga cikin al’ummata ta salla ta riske shi ya yi ta (a ko’ina ne)” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Hikimar Shar’anta Taimama

1 - Sauwaqawa al’ummar Muhammad ( صلى الله عليه وسلم )

2 - Kawar da cutar da za ta faru saboda amfani da ruwa a wasu lokutan, kamar lokacin rashin lafiya, ko tsananin sanyi, da makamancin haka.

3 - Dauwama a kan ibada, da rashin yanketa saboda yankewar ruwa

Yaushe Shari’a Ta Ba Da Damar A Yi Taimama

1 - Yayin rashin ruwa

Saboda faxin Allah Ta’ala : “Ba ku samu ruwa ba, ku yi taimama” (Alma’ida : 6).

Ba a cewa mutum ya rasa ruwa, idan bai neme shi ba.

2 - Yayin Kasa Amfani Da Ruwa, Koda Akwai Shi.

Kamar marar lafiya ko tsohon da ba zai iya xauko ruwan ba, kuma babu wanda zai taimaka masa wajen yin alwalar.

Marar lafiya
Tsoho

3 - Yayin Tsoron Kamuwa Da Wata Cuta Idan An Yi Amfani Da Ruwan

- Kamar :

A - Mara lafiyan da idan ya yi amfani da ruwan ciwonsa zai qaru.

B - ko mutumin da yake jin tsananin sanyi, kuma bai da abin da zai xumama ruwa da shi, sannan yana kyautata zaton idan ya yi wanka da ruwa cuta za ta kama shi. “Saboda abin da ya tabbata Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya tabbatar da Amru xan Asi a kan abin da ya yi, yayin da ya yi wa abokansa sallah, bayan ya yi taimama saboda tsananin sanyi”[ Abu Dawud ne ya rawaito shi].

C - Idan yana wani wuri mai nisa, kuma babu ruwa a tare da shi sai xan kaxan, wanda yake buqatarshi wajen sha, ga shi ba zai iya samo wani ba (sai ya yi taimama)

Yadda Ake Taimama

1 - Ya doki qasa da hannayensa biyu bugu xaya.

2 - Sannan ya bushe su don ya rage qurar da take kansu

3 - Sannan sai ya shafi fuskarsa da hannayensa sau xaya

4 - sannan sai ya shafi bayan tafin hannunsa, ya shafi bayan tafin hannun dama da cikin hannun hagu, sannan bayan hagu da cikin hannun dama.

Dalilin wannan siffar ta taimama shi ne hadisin Ammar - Allah ya qara yarda da shi - ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya doki qasa da tafin Hannayensa biyu, ya busa a cikinsu, sannan ya shafi fuskarsa da hannayensa da su” [Bukhari Da Muslim ne suka rawaito shi].

Farillan Taimama

1 - Niyya

2 - Shafar Fuska

3 - Shafar Tafuka

4 - Jerantawa : ya fara da fuska sannan tafukan hannu

5 - bi-da-bi : ya shafi hannayensa kai tsaye bayan ya shafi fuskarsa.

Abubuwan Da Suke Vata Taimama

1 - Samuwar ruwa

2 - Faruwar wani abu da yake warware alwala, kamar yin tusa

3 - Faruwar wani abu da yake wajabta wanka, kamar mafarki

4 - Gushewar uzurin da saboda da shi ne aka shar’anta taimama, kamar rashin lafiya ko makamancinta.

Ya halatta a yi taimama a kan darduma ko cafet
Taimama
Wanda ya rasa qasa
Wanda ya rasa ruwa
Ya tabbata a ilimin kimiyya
cewa a cikin turvayar qasa akwai wani abu mai tsarki, wanda yake kashe dukkan wasu qwayoyin cuta kowane iri ne.

Mas’aloli

1 - Yin sallah da taimama yayin rashin ruwa, shi ya fi akan mutum ya yi sallah da alwala amma yana jin fitsari ko bayan-gida.

2 - Ya halatta a yi taimama a kan bango ko darduma idan akwai qasa ko qura a kansu.

3 - Ya halatta ga wanda ya yi taimama ya sallaci abin da ya so na sallolin farilla da nafila, matuqar bai yi abin da yake warware taimama ba.

4 - Ya halatta mai alwala ya bi mai taimama sallah, saboda tabbatarwar da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم )“ya yi wa Amru xan Asi lokacin da ya yi wa abokansa sallah, alhali ya yi taimama saboda tsananin sanyi” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

5 - Wanda ya yi taimama ya yi sallah, sannan ya samu ruwa kafin fitar lokaci, ba zai sake wannan sallar ba.

An karvo daga Abu Sa'id Alkhudriy - Allah ya yarda da shi - ya ce, “Wasu mutane biyu sun yi tafiya, sai lokacin sallah ya yi, kuma ba su da ruwa, sai suka yi taimama a wuri mai tsarki suka yi sallah, sannan sai suka samu ruwa a kan lokaci, sai xayansu ya yi alwala ya yi sallah, xayan kuma bai rama ba. Sannan suka zo wajen Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) suka faxa masa, sai ya ce wa wanda bai sake ba, “Ka dace da sunnah, sallarka ta isar maka”. Ya ce wa wanda ya yi alwala ya yi sallah “Kana da lada sau biyu” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

6 - Wanda ya yi taimama, sai kuma ya samu ruwa, kafin ko yana cikin sallah, to wajibi ne a kanshi ya yi alwala, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Wuri mai tsarki tsarkin mumini ne, ko da kuwa bai samu ruwa ba tsawon shekara goma, idan ya samu ruwa to ya shafa shi ga fatar shi (ya yi wanka) wannan shi ne ya fi alheri” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

7 - Babu wani abin da zai hana musulmi sallah, haka kuma kada ya jinkirta daga lokacinta, idan ba zai iya amfani da ruwa ba, ko bai samu ruwa ba, ya yi taimama, idan ya kasa yin taimamar ya yi sallar haka nan ba da alwala ba.

8 - Wanda ya rasa ruwa da qasa, to ya yi sallah a kan lokacinta ba tare da tsarki ba, kuma ba sai ya sake ba, saboda Allah ya ce, “Ku ji tsoron Allah daidai iyawarku” (Attagabun : 16)

9 - Ya halatta wanda yake sa ran zai samu ruwa ya jinkirta taimama zuwa qarshen lokaci. Amma idan ya xebe qauna ga samun ruwa, to abin da aka fi so ya gabatar da sallar shi a farkon lokaci, saboda sallah a farkon lokaci ta fi falala.

10 - Idan mutum ya ji tsoron fitar lokaci, ya yi taimama alhali ga ruwa nan, to wannan aiki bai yi ba, wajibi ne a kanshi ya yi alwala koda lokaci zai fita.Tags: