Ita ce, Kyau da tsafta
Ita ce, Kyau da tsafta
Ita ce, amfani da ruwa a kan kevantattun gavvai da niyyar tsarki
Ko dai alwala ta zama wajibi ko mustahabbi :
Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ya ku waxanda suka yi imani idan kun tashi za ku yi sallah ku wanke fuskokinku da hannayenku zuwa gwiwowin hannu, ku shafi kawunanku, ku wanke qafafuwanku zuwa idan sawu” (Al’ma’ida : 6)
Saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) ga matar da take al’ada “Kada ki yi xawafi har sai kin tsarkaka” [ Bukhari ne ya rawaito shi].
Saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Ba mai shafarsa sai waxanda aka tsarkake” (Alwaqi’a : 79)
Saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Ba wanda yake kiyaye yin alwala sai mumini” [Ahmad ne ya rawaito shi] Ana matuqar son jaddada alwala lokacin yin kowace sallah, da lokacin zikiri da addu’a, da yayin karatun Alqur’ani, da gabanin yin barci, da gabanin yin wanka, da bayan xaukar gawa, da duk lokacin da mutum ya yi kari, koda ba lokacin sallah ba ne.
Allah Ta’ala ya ce, “Haqiqa Allah yana son masu tuba yana son masu yin tsarki” (Albaqara : 222)
Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Haqiqa Al’ummata zasu zo ranar alqiyama suna masu fari a goshi da qafafuwa [ Farin goshi da qafafuwa, ana nufin hasken da wuraren alwala za su yi ranar alqiyama.] saboda yin alwala, duk wanda ya samu ikon qara tsawon farin goshinsa daga cikinku to ya yi” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda duk ya yi alwala ya kyautata alwalar, laifukansa zasu fita daga jikinsa, har ta qarqashin Faratansa” [Muslim ne ya rawaito shi]
Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Bana nuna muku abin da Allah yake kankare zunubai da su ba? Sai suka ce, “E, ya Manzon Allah, sai ya ce, “Kyautata alwala akan dole [ A kan dole : Ma’anarsa abin da yake mutum ba ya son shi, kuma yana wahalar da shi.], yawaita tafiya zuwa masallatai, jiran sallah bayan an yi sallah, wannan shi ne ribaxi” [ Muslim ne ya rawaito shi].
1 - Halarto da niyya a cikin zuciya
2 - Ambaton sunan Allah, ya ce, «Bismillah»
3 - Wanke tafukan hannu sau uku
4 - Yin asuwaki, yayin kurkure baki
5 - Kurkuran baki, shaqa ruwa da facewa (Sau uku)
Kurkure baki shi ne, sanya ruwa cikin baki tare da jujjuya shi.
Shaqa ruwa : shi ne shaqar ruwa zuwa ga hanci
Ana kurkuran baki da shaqa ruwa daga kamfata xaya.
Facewa, shi ne fato ruwa daga hanci.
6 - Wanke fuska (Sau uku) tare da tsetstsefe gemu.
Iyakar fuska shi ne daga mafarin gashin kai zuwa qasan hava. Faxi kuma daga kunne zuwa kunne.
7 - Wanke hannun dama, tun daga saman ‘yan yatsu zuwa gwiwar hannu, sau uku, haka ma hannun hagu.
8 - Shafar kai, a jiqa hannu da ruwa, sannan a shafi farkon kai zuwa qeya, sannan a dawo farkon kai inda aka fara, (Sau xaya).
9 - Shafar cikin kunne da xan yatsa manuniya, da shafar bayan kunne da babban xan ‘yatsa (Sau xaya)
10 - Wanke qafar dama zuwa idon sawu (sau uku) haka qafar hagu ita ma sau uku
11 - Yin addu’a bayan an gama alwala, a ce, “Ashhadu An la ilaha illal lahu, wahdahu La sharika Lahu, Wa Ash hadu Anna Muhammadan Abduhu Wa Rasuluhu” [ Muslim ne ya rawaito shi] “Allahummaj ‘alni Minat Tawwabina, Waj Alni Minal Mutaxahirina” [ Tirmizi ne ya rawaito shi] “Subhanakallahumma Wabi hamdika, Ash Hadu Alla ilaha Illa Anta, Astagfiruka Wa a tubu Ilaika” [ Nasa’i ne ya rawaito shi].
1 - Ruwan ya zama mai tsarkakewa
2 - Ya zama ruwan halal ne, ba kamar wanda aka sato ba.
3 - A kawar da duk abin da zai hana ruwa isa ga fata, kamar fanti da makamancinsa.
1 - Yin niyya a cikin zuciya, ba a faxinta da baki, da mutum zai yi abubuwan da ake yi wajen alwala da niyyar ya ji sanyi, ko don ya tsaftace jikinsa ba tare da ya yi niyyar alwala ba, to da wannan abin da ya yi bai isar masa ba.
2 - Wanke fuska, haxe da kurkure baki da shaqa ruwa
3 - Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu
4 - Wanke qafafu haxe da idon qafa
5 - Shafar dukkan kai, haxe da shafar kunnuwa
6 - Jerantawa tsakanin gavvai (wato wanke su a jere)
7 - Wanke gavvai xaya bayan xaya, kada ya jinkirta wata gava har ta bushe, bai wanke wadda take bin ta ba.
1 - Wanke tafukan hannu sau uku a farkon alwala
2 - Yin asuwaki
3 - Wanke gavvai sau uku-uku, ban da kai da kunnuwa, su ba a qara wa a kan sau xaya.
4 - Farawa da dama a dukkan gavvan alwala
5 - Tsawaita farin hannaye, ma’ana ya qara shigo da gwiwar hannu wajen wankewa
6 - Tsetstsefe gemu, don isar da ruwa zuwa ga fatar hava
7 - Tsatstsefe tsakanin ‘yan ‘yatsun hannu da qafafuwa
8 - Cuccuxa gavvan hannu, kada ya wadatu da yayyafa ruwa kawai
9 - Taqaita zubar da ruwa, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Za a samu wasu a cikin wannan al’umma suna wuce iyaka a wajen tsarki” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].
Ma'ana suna varna a wajen ruwan alwala
10 - Yin addu’a bayan gama alwala, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Babu wani daga cikinku da zai yi alwala, ya kyautata alwalar, sannan ya ce, “Ashhadu An la ilaha illal lahu, Wa Ash hadu Anna Muhammadan Abduhu Wa Rasuluhu” “Allahummaj ‘alni Minat Tawwabina, Waj Alni Minal Mutaxahirina” Face sai an buxe masa qofafin Aljannah guda takwas, ya shiga ta wadda ya ga dama” [Tirmizi ne ya rawaito shi].
11 - Yin sallah raka'a biyu bayan gama alwala, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda duk ya yi alwala irin alwalata wannan, sannan ya tashi ya yi raka’a biyu, bai zancen zuci a cikinsu ba, face sai an gafatar masa abin da ya gabata na zunubansa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
1 - Dukkan abin da yake fita daga mafita biyu, fitsari [ Mafita guda biyu, su ne gaban mutum da dubura.], bayan-gida, tusa, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Allah ba ya karvar sallar xayanku idan ya yi kari, har sai ya yi alwala” [Muslim ne ya rawaito shi.]
2 - Barci mai nauyi, wanda ba a jin komai a cikinsa, hakanan dukkan abin da ya yi kama da shi, kamar suma da gusar da hankali gabaxaya.
3 - Cin naman Raqumi, saboda hadisin Jabir xan Samura ya ce, wani mutum ya tambayi Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) cewa “Za mu sake alwala idan mun ci naman raqumi? Sai ya ce, “E, (za ku sake) [ Muslim ne ya rawaito shi].
4 - Shafar farji da hannu kai tsaye ba tare da wata kariya ba, saboda hadisin Busrata yar Safwan ta ce, ta ji Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana cewa, “Duk wanda ya shafi gabansa to ya (sake) alwala” [ Abu Dawud ne ya rawaito shi].
1 - Idan musulmi ya tashi daga barcin, kuma ya yi nufin ya yi alwala da kwano ko kwarya, to kada ya kamfata da hannayensa har sai ya wanke su sau uku, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan xayanku ya farka daga barcinsa, kada ya tsoma hannunsa a cikin qwaryarsa, har sai ya wankesa sau uku, domin bai san a ina hannunsa ya kwana ba” [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
2 - Wajibi mai yin alwala ya yi qoqarin sadar da ruwa ga dukkan gavovinsa, waxanda ya wajaba ya wanke su, musammam ma tsakanin 'yan 'yatsunsa na qafafu da hannaye, da tsakanin saje da kunne, da gwiwowin hannu da idon qafa da digadigansa [ diddige: Tudun naman dake bayan tafin qafa.], saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Azaba ta tabbata ga wasu digadigai daga wuta” [ Muslim ne ya rawaito shi].
3 - Asali shi ne gina komai a kan yaqini, (misali) da zai tabbatar yana da tsarki, sannan ya yi shakka a kan cewa alwalarsa ta warware ko kuwa? To sai ya yi gini akan yaqini, wanda shi ne tsarki. (ma’ana zai tafi akan yana da tsarki).
Haka kuma idan ya tabbatar bai da tsarki, amma sai ya yi shakka ya yi alwala ko bai yi ba? To yaqini anan shi ne bai da tsarki.
4 - Idan musulmi ya yi alwala ya wanke gavvan alwala sau xai-xai, ko sau biyu-biyu, ko ya wanke wasu sau xaya, wasu sau biyu, wasu sai uku, to alwalarsa ta inganta.
5 - Wanda ya manta ya yi sallah ba tare da alwala ba, to ya wajaba a kanshi ya sake, a duk lokacin da tuna.
6 - idan ya yi alwala, sai najasa ta same shi, to zai gusar da najasar ne ba zai sake alwalar ba ne, saboda ba kari ba ne ya yi..
1 - Faxin niyya a fili yayin alwala
2 - Varnar ruwa
3 - A qari akan wanki uku a wajen alwala, saboda hadisin da aka rawaito wani mutumin qauye ya zo wajen Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) yana tambayarsa yadda ake alwala, sai ya nuna masa wanki uku-uku, sannan ya ce, “Haka ake alwala, duk wanda ya qara a kan haka, to ya munana aiki, ya wuce gona da iri, ya yi zalunci” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].
Sai dai ya halatta a qara a kan wanki uku idan gavar ba ta wanku ba, kamar wanda a hannunsa akwai mai ko makamancinsa
4 - Rashin kyautata alwala, saboda an rawaito cewa “wani mutum ya yi alwala, ya bar wani xan wuri daidai faxin farce a qafarsa bai wanke ba, sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya gan shi, sai ya ce masa, “Koma ka kyautata alwalarka” sai ya koma ya kyautata, sannan ya zo ya yi sallah ”[Muslim ne ya rawaito shi].
- Yana Daga Rashin Kyautata Alwala :
a) Rashin wanke idanuwan qafa
b) Rashin wanke gwiwowin hannu, saboda matsewar hannun riga
c) Rashin wanke xan wurin da yake tsakanin saje da kunne.
d) Mutum ya yi lawala alhalin jikinsa da xige-xigen fanti.
e) Rashin wanke tafin hannun hagu tare da hannun hagun.
f) Mace ta yi alwala alhali a ‘yan ‘yatsunta akwai abin da yake hana ruwa isa.
g) Rashin tsetstsefe ‘yan ‘yatsun qafa, a yayin da ruwa ba shiga cikinsu.
5 - Shafar wuya : Shafar wuya ba ya cikin alwala, sai dai idan akwai buqatar ya shafi wuyan kafin ko bayan gama alwala to babu laifi.
6 - Faxin zikirin da bai zo a shari’a ba, kamar
- Yin kevantacciyar addu’a yayin wanke kowace gava.
- Faxin "Zamzam" ga wanda yake alwala.