Hukunce-Hukuncen Najasa

22916

Bayanin najasa

Abin da ake nufi da najasa a larabci

Qazanta

Ma’anar najasa a shari’a

Qazantar da shari’a ta yi umarni da a gusar da ita

Nau’ukan Najasa

1 - Bawalin Xan Adam Da Bayan Gidansa

Saboda hadisin mutumin qauyen da ya yi fitsari a cikin masallaci, sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce masa, “Waxannan masallatai bai dace a yi fitsari ko qazanta a cikinsu ba, An gina su ne kawai don ambaton Allah da sallah da karatun Alqur’ani”. [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

2 - Jinin Haila

Saboda abin da ya tabbata cewa Khaulatu ‹yar Yasar cewa ta zo wajen Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ta ce masa “Ya Rasulallahi, ban da tufa sai guda xaya, ga shi kuma ina yin al’ada a cikinta” Sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce da ita “Idan kin tsarkaka ki wanke wurin jinin, sannan ki sallah da ita”. [ Abu Dawud ne ya rawaito shi]

Duk jinin da ba na haila ba ne mai tsarki ne. mai kwarara ne ko marar kwarara [ Jini mai kwarara shi ne wanda yake fita daga mahallinsa yana zuba.], saboda abin da ya tabbata cewa wani “ arne ya harbi wani musulmi yana sallah da kibiya, ya same shi, sai ya cire kibiyar ya ci gaba da sallarsa, alhali jini yana zuba daga jikinsa. ”[ Abu Dawud ne ya rawaito]

3 - Fitsari Da Kashin Dabbar Da Ba A Cin Namanta

Saboda hadisin Abdullahi xan Mas’ud – Allah ya yarda da shi – ya ce, “ Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya je wajen bayan-gida, sai umarce ni in kawo masa duwatsu guda uku, sai na samu biyu, na nemi na ukun ban samu ba, sai na xauko kashin dabbobi na zo masa da shi, sai ya karvi duwatsun guda biyu, ya jefar da kashin dabbobin ya ce, “Wannan qazanta ne ”. [ Bukhari ne ya rawaito shi.]

Menene hukuncin fitsari da kashin dabbar da ake cin namanta?
Fitsari da kashin dabbar da ake cin namanta mai tsarki ne, saboda abin da ya tabbata daga Anas xan Malik Allah ya yarda da shi ya ce, wasu mutane sun zo Madinah, sai suka yi ta rashin lafiya, sai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya aika su waje raquman sadaka don su riqa shan fitsarinsu da nononsu. [ Bukhari ne ya rawaito shi.]

4 - Mushe

Shi ne abin da ya mutu da kansa ba tare da yanka na shari’a ba, saboda faxin Allah Mai girma da buwaya : “Ka ce, ban samu abin da yake cinsa haramun ba ne cikin abin da aka yi min wahayinsa, sai dai in mushe ne ko jinin da yake kwarara ko naman alade, haqiqa shi qazanta ne”. (Al’an’am : 145).

Mushe ya haxa abin da aka yanko daga jikin dabba mai rai kafin a yanka ta.

Mushe

Sai dai an togace abubuwa kamar haka:

1- Mushen Kifi Da Na Fara

Saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “An halatta mana mushe biyu, da jini biyu, mushe biyu su ne, mushen kifi da mushen fara, jini biyu kuma su ne, hanta da saifa”.[ Ahmad ne ya rawaito shi]

Kifi
Fara

2- Mushen Abin Da Jini Ba Ya Gudana A Jikinsa Kamar Quda

Saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) : “Idan kuda ya faxa a cikin kwanon xayanku, to ya dulmiya shi gabaxayansa, sannan ya cire shi ya jefar, saboda a fiffikensa xaya akwai waraka, a xayan kuma akwai cuta”. [ Bukhari ne ya rawaito shi.]

Quda

5 - Naman Alade

Saboda faxin Allah mai girma da buwaya : “ Ka ce, ban samu abin da yake cinsa haramun ba ne cikin abin da aka yi min wahayinsa, sai dai in mushe ne ko jinin da yake kwarara ko naman alade, haqiqa shi qazanta ne” (Al-anam : 145)

Alade

6 - Kare

Kare gabadayansa najasa ne, najasar yawunsa kuma mai tsanani ce, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Tsarkin kwanon xayanku idan kare ya yi lallage a cikinsa, shi ne ya wanke shi sau bakwai, ya sa qasa a wanki na farko”.[Bukhari da Muslim ne suka rawaito]

Abin da ake kira lallage shi ne, kare ya sanya harshensa ya jujjuya shi a cikin kwano, ko ya sha abin da yake ciki, ko bai sha ba.

Abin da kare ya sha ya rage

7 - Maziyyi

Shi wani ruwa ne fari, ba shi da kauri kuma yana da danqo, yana fita yayin wasa da mace, ko kuma tunanin jima’i, ba ya fita da sha’awa ko tunkuxar juna, ba a jin mutuwar jiki bayan fitarsa, wani lokacin ma ba a sanin lokacin da yake fita.

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce da Aliyyu xan Abu Xalib (R.A) lokacin da ya yi masa tambaya game da Maziyyi, ya ce masa : “Ka wanke gabanka, ka sake alwala”. [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito]

8 - Wadiyyi

Shi wani ruwa ne fari, mai kauri, yana fita bayan fitsari.

Maniyyi mai tsarki ne

Maniyyi: wani ruwa fari, mai kauri, yana fitowa tare da sha'awa, yana tunkuxar juna, ana samun mutuwar jiki bayan fitarsa, yana wari irin wari bara-gurbin qwai.

Maniyyi mai tsarki ne, domin da najasa ne da Manzon Allah (r) ya yi umarni a wanke shi.Ana wanke shi in yana xanye, in ya bushe kuma to kawai sai a kankare shi, saboda hadisin A'isha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “ Manzon Allah (r) ya kasance yana wanke maniyyi, sannan ya fita zuwa sallah da wannan tufar, ina gani gurbin wurin da ya wanke”. [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito]

A riwayar Muslim : “Na gan ni ina kankare shi (maniyyi) daga tufar Manzon Allah (r) sosai, sannna ya yi sallah da wannan tufar”. [Muslim ne ya rawaito shi]

Kankare maniyyi idan ya bushe
Wanke maniyyi idan yana xanye
Giya da Turare

Giya ba najasa ba ce, duk da cewa qazanta ce, kuma shanta yana daga cikin manya-manyan zunubai, sai dai babu wani dalili da ya nuna cewa najasa ce.

Faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Yaku waxanda suka yi imani ku sani cewa lallai giya da caca da gumaka da rantsuwa da kibau qazanta ne daga aikin Shaixan don haka ku nisance su ko kun rabauta” (Al-ma'ida :90)

Abin da ake nufi da qazanta a nan shi ne qazanta da voye ba ta fili ba, kamar yadda caca da gumaka suke qazanta amma ba ta zahiri ba .

Da wannan ne zamu gane halaccin amfani da turaren da suke da alkaohol a cikinsu, saboda shi Alkahol ana samu shi ne daga giya.

Giya da Turare

Hanyoyin Tsarkaka Daga Najasa

1 - Tsarkin Qasa Mai Najasa

Idan najasa ta samu qasa, to wannan najasa tana gushewa ne da ruwa ko waninsa, saboda hadisin mutumin qauyen nan da ya yi fitsari a masallaci, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Ku qyale shi, ku kwarara ruwa guga xaya akan fitsarinsa, ko ku zuba guga babba ta ruwa”.[ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

Idan kuwa najasar ruwa ce, ta bushe to ta tsarkaka, saboda hadisin Abu Qilaba – Allah ya yarda shi – ya ce, “Idan qasa ta bushe to ta tsarkaka [ Ta tsarkaka ]” [ Bukhari ne ya rawaito shi].

Wanke qasa da ruwa
Najasa mai kwarara akan qasa
Najasar da ta kwarara ta bushe

2 - Tsarkake ruwa Mai najasa

Yana tsarkakuwa idan aka haxa shi da wani ruwan mai yawan da zai gusar da alamar najasar, kamar yadda yana tsarkakuwa idan aka tace da na’urorin zamani da ake tace ruwa da su.

Tsarkakewa ta hanyar na’urar zamani
Tsarkakewa ta hanyar qara ruwa

3 - Tsarkake Tufa Mai Najasa

Ana wanke ta da ruwa, a kankare, a matse, har najasar ta gushe.

Tsarkake Tufa mai najasa

4- Tsarkake Shimfixa

Ana wanke wa da ruwa, ko kuma da abubuwan tsaftace wa na zamani, kuma a kankare, har najasar ta gushe.

Tsarkake shimfixu

5 - Tsarkake Fatar Mushe

1- Fatar Mushen Dabbar Da Ake Cin Namanta

Ana tsarkake ta da jima, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan aka jeme fata [ Fata : fatar da ba a jeme ba ] to ta tsarkaka” [ Muslim ne ya rawaito shi].

Jima ita ce, sanyawa fata wasu sinadarai waxanda za su sa ta yi laushi, ta daina wari.

Idan kuwa dabbar da ake ci ba mushe ta yi ba, yanka ta aka yi ta hanyar da shari’a ta amince, to fatarta mai tsarki ce.

2- Fatar Mushen Dabbar Da Ba A Cin Namanta

(Fatar wannan dabbar) tana xaukar hukuncin mushe, ba ta tsarkaka, ko da an yanka dabbar ta hanyar shari’a.

Wata dabba da ake cin namanta
Jima
Wata dabba da ba a cin namanta

6 - Tsarkake fitsarin yarinya, da fitsarin yaron da bai fara cin abinci ba

Ana wanke fitsarin yarinya, amma fitsarin yaro ana yayyafa ruwa ne kawai, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Ana wanke fitsarin yarinya, ana yayyafa ruwa fitsarin yaro ne” [ Abu Dawud ne ya rawaito shi.].

Yayyafa ruwa akan fitsarin yaro
Wanke fitsarin yarinya

7- Tsarkake abin da kare ya yi lallage acikinsa

Ana wanke wa sau bakwai, na farko da qasa, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Tsarkin kwanon xayanku idan kare ya yi lallage a cikinsa, a wanke shi sau bakwai, na farko da qasa” [Bukhari Da Muslim ne suka rawaito shi].

Tsarkake wa da qasa (Sau xaya) Sannan Tsarkakewa ta hanyar wanke wa (Sau shida)

8- Tsarkake Maziyyi da Wadiyyi

Zai wanke gabansa, ya yi alwala, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) a cikin hadisin Aliyu xan Abu Xalib – Allah ya yarda da shi – “Ka wanke gabanka, ka yi alwala” [ Bukhari Da Muslim ne suka rawaito shi].

Ita kuwa rigar (da wadiyyi ko maziyyi ya tava) sai kawai ya yayyafa ruwa a wurin da maziyyin ko wadiyyin ya tava, saboda hadisin Sahli xan Hunaif, ya tambayi Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Na ce ya Manzon Allah ya ya zanyi da abin da ya tava tufa ta na maziyyi da wadiyyi, sai ya ce, ya isa ka xebi tafi xaya na ruwa ka yayyafa wa tufafinka, Inda kake ganin ya tava” [ Abu Dawud ne ya rawaito shi].

9- Tsarke jinin haila

Ana wanke wa da ruwa, abin da ya rage na alamansa ba ya cutarwa, saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Ruwa ya wadatar miki, alamar (jini) ba za ta cutar dake ba” [ Abu Dawud ne ya rawaito shi].

10- Tsarkake takalmi

Ana goga shi akan qasa ne, har sai najasar ta tafi, saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan xayanku ya taka qazanta da takalminsa, qasa tana tsarkake shi”.[ Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Tsarkake takalmi ta hanyar gurza shi a qasa

11- Tsarkake doguwar rigar mata

Idan wani abu na najasa ya maqale a cikin rigar mace, tafiyar da take a wuri mai tsarki yana isar mata, qasa tana tsarkake ta, saboda faxinsa ( صلى الله عليه وسلم ) “Abin zai biyo bayansa yana tsarkake shi” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Yadda qasa take tsarkake tufar mace

12- Tsarkake abincin da yake daskararre

Ana tsarkake shi ta hanyar xebe najasar da inda ta tava a zubar da ita, abin da ya rage yana nan da tsarkinsa, saboda abin da “ya tabbata Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) an tambaye shi akan vera idan ya faxa kakide, sai ya ce, “Ku jefar da veran da gefen wurin, ku ci (Sauran) manku” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Daskararren mai da vera matacce ya faxa cikinsa

13- madubi da kwalba

Ana gogewa ne har alamun najasar su gushe

Tsarkake gilas ta hanyar gogewa
Mas’aloli akan najasa

1 – A qa’ida duk wani abu mai tsarki ne, sai idan dalili ya nuna najasa ne.

2 – Idan najasa ta faxa akan wani abu, aka kasa gane inda ta faxa, to sai a wanke abun gabaxaya.

3 – Idan najasa ta zama wani abu daban, kamar a qona kashin jaki ya zama toka, to ya zama mai tsarki.



Tags: