Ziyarar Madinah, Falalarta Da Matsayinta

7258

Sunayen Madinah

1 – Al-madinah,

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Suna cewa idan muka koma Madinah maxaukaka za su fitar da maqasqanta daga cikinta”. (Al-munafiqun : 8).

2 – Xaba :

An karvo daga Jabir xan Samura – Allah ya yarda da shi – ya ce, na ji Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana cewa : “Haqiqa Allah Ta’ala ya kira Madinah da Xaba” [Muslim ne ya rawaito shi]

3 – Xaiba :

An karvo daga Zaid xan Sabit – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Haqiqa (Madinah) Xaibah ce, tana kore zunubai kamar yadda wuta take kore dattin Azurfa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

Falalar Garin Madinah

1- An karvo daga Sa’ad xan Waqqas – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Madinah ta fi musu alheri da sun sani, babu wani wanda zai barta don baya sonta face sai Allah ya canza wanda ya fi shi alheri a cikinta Ba kuma wanda zai tabbata a cikinta, duk da quncin rayuwa da wahalar dake cikinta, face sai na zama mai cetonsa ko mai shaida a kansa ranar alqiyama” [Muslim ne ya rawaito shi]

2- An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “An umarce ni (da yin hijira zuwa) wata alqarya da take cinye alqaryu, suna ce mata Yasrib, ita ce Madinah, tana kore mutanen (banza) daga cikinta, kamar yadda wutar qira take kore dattin qarfe” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

Wasu Daga Cikin Abubuwan Da Madina Ta Kevanta Da Su

1 – Tsakanin Dutsen Airu da Sauru da suke Madinah harami ne, an hana sare bishiyar wurin da yin farauta a wurin.

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, «Madina harami ce tsakanin dutsen Airu da Sauru, duk wanda ya qirqiri wani abu a cikinta, ko ya voye mai laifi, to tsinuwar Allah da Mala’iku da mutane ta tabbata a kanshi” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

Dutsen Sauru
Dutsen Airu

2 – Ana ninnika ladan sallah a cikin Masallacin Madina.

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Sallah a masallaci na wannan, ta fi sallah dubu a wani masallacin daban, sai dai in masallacin Haramin Makkah ne” [Bukhari ne ya rawaito shi]

3 – A cikin ta akwai Dausayi (rauda) daga dausayin Aljannah, sunna ce yin sallah a cikinsa. An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Tsakanin gidana da minbarina dausayi ne daga cikin dausayin aljannah Minbarina yana kan tafkina” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

Rauda (Dausayin Aljannah A Masallacin Annabi)

4 – Dujal ba zai shige ta ba a qarshen zamani, haka ma annoba bata shigarta.

An karvo daga Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Dujal zai zo Madina, sai ya samu Mala’iku suna gadinta Dujal ko annoba ba za su shiga Madina ba insha Allahu” [Tirmizi ne ya rawaito shi]

5 – Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya roqa mata albarka.

An karvo daga Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce,“Ya Allah ka sanya ninkin abin da ka sanya na albarka a Makka a cikin Madina” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

Hukuncin Ziyarar Masallacin Annabi ( صلى الله عليه وسلم )

Ziyarar masallacin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ba ta cikin sharuxxa ko rukunai ko wajiban aikin hajji, sunna ce, kuma an shar'anta ziyarar a kowanne lokaci.

Wajibi ne niyyar ziyarar ta zama don yin sallah ne a Masallacin ba don qabari ba. An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Ba a niqar gari a tafiya sai don zuwa masallatai guda uku, masallacin harami, masallacin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) da masallaci mai nisa (Qudus)”.[Muslim ne ya rawaito shi]

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya ya ce, "Idan Manufar tafiyarsa ita ce ziyarar qabarin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ba sallah a masallacinsa ba…..to abin da mafi yawancin malamai suke tafi a kai shi ne ba shar'anta hakan ba, ba a yi umarni da hakan ba….hadisan da suka zo a kan ziyarar qabarin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) dukkaninsu masu rauni ne da haxuwar malaman hadisi, kai hadisai ne ma na qarya, babu wani cikin malamai masu littattafan "Sunan" da ake dogara da su da ya rawaito su, kuma babu wani malami da ya yi hujja da su".[Duba littafin "Majmu'ul Fatawa" Juzu'i na 27 shafi na 26]

Hukunce-Hukuncen Ziyara Da Ladubbanta

1 – Idan mai ziyara ya isa masallacin, sunna ne ya gabatar da qafarsa ta dama yayin shiga, ya ce, “Allahummaf tah li abwaba rahmatika" Ma'ana "Ya Allah ka buxe min qofofin rahamarka”. [ Muslim ne ya rawaito shi]

2 – Zai yi sallah raka'a biyu gaisuwar masallaci, idan ya yi su a cikin Rauda to shi ya fi falala.

3 – Sunna ce ziyarar qabarin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) da abokansa biyu Abubakar da Umar, ya tsaya daidai qabarin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) cikin ladabi da rage murya, ya yi salati gare shi, sannan ya yi sallama ga Abubakar sannan umar.

4 – Sunna ne mai ziyara ya sallaci salloli biyar a masallacin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ), ya yawaita ambaton Allah da roqonsa, da sallar nafila, musammam ma a cikin Rauda.

5 – Sunna ce ya ziyarci masallacin Quba don yin sallah a cikinsa, idan ziyarar ta shi ta zama ranar assabar to hakan shi ya fi, saboda hadisin Abdullahi xan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana zuwa quba, akan abin hawa ko a qafa, ya yi sallah raka’a biyu a cikinsa” A wani lafazin “Yana nufin yana zuwa quba duk ranar assabar” [Muslim ne ya rawaito shi]

6 – Sunna ce ziyartar maqabartar Baqi’a, da maqabartar waxanda suka yi shahada, da qabarin Hamza, saboda Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) yana ziyartarsu, yana musu addu’a, yana cewa : “Assalamu Alaikum Ahlal Diyar Minal Mu’uminina Wal Muslimina, Wa Inna Insha Allahu Bikum Lahiquna, Nas’alullaha Lana Walakumul Afiya” Ma’ana : “Amincin ya tabbata a gareku masu gidaje, muminai da musulmai, muma – insha Allahu- zamu tarar da ku, muna roqon Allah lafiya mu da ku gabaxaya” [Muslim ne ya rawaito shi]

Kura-kurai Da Faxarkarwa A Kan Ziyara

1 – Bulagoro da niqar gari da niyyar ziyarar qabari, da wuraren tarihi a Madinah. Abin da aka shar’anta niqar gari saboda shi, shi ne ziyarar Masallacin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) da yin sallah a cikinsa, ziyarar qabari tana shigowa a cikinsa.

2 – Fuskanta qabari yayin addu’a.

3 – Roqon Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) da neman biyan buqatu a wajensa, ba a wajen Allah ba, wannan shirka ce babba.

4 – Shafar bangon xakin da qabarin Annabi yake ciki don neman albarka, wannan bidi’a ce haramtacciya, kuma hanya ce daga hanyoyin shirka.

5 – Xaga Murya a wajen qabarin Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) da daxewa a wurin a tsaye, da maimata sallama daga nesa duk lokacin da ya shiga, da xora hannun dama a kan na hagu a kan qirji lokacin sallamar, kamar mai sallah.

Wasu Daga Cikin Falalar Madinah
An karvo daga Abdullahi xan Zaid, ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Haqiqa Annabi Ibrahim ya haramta Makkah ya yi mata addu’a, ni kuma na haramta Madina kamar yadda (Annabi) Ibrahim ya haramta Madinah, na yi mata addu’a, a cikin mudinta da sa’inta, kamar yadda Ibrahim (AS) ya yi wa Makkah addu’a” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].


< 10 Layya Layya

Tags: