Aikin Hajji Da Talbiyya

4665

Aikin Hajji

Bayanin Mene ne Aikin Hajj

Kalmar "Annuskhu" ma’anar ta da larabci shi ne:

Gudun duniya da Ibada

Annuskhu a Shari'a shi ne

Abin da Alhaji ko mai umara yake faxa ko yake aikata wa.

Niyyar Aikin Hajji

Idan maniyyaci ya gama wankansa da tsaftarsa, ya sanya kayan ihraminsa, namiji ya cire duk wani xinkakken abu, sai ya yi niyyar shiga aikin hajj ko umara. Ana so ya faxi irin aikin da ya yi niyya,

misali idan ya yi niyyar umara sannan ya zarce aikin hajji sai ya ce, «Labbaikal Lahumma Ummaratan Mutamatti’an Biha Ilal Hajj» (Ma’ana : Ya Allah na amsa maka da umara ina mai wuce wa da ita zuwa hajji).

Ko kuma ya ce, «Labbaikal Lahumma Umratan» (Ma’ana : Ya Allah na amsa maka da Umara» ko kuma idan hajji ne kaxai zai yi sai ya ce, “Labbaika Hajjan” (Ma’ana Ya Allah na amsa maka da hajji) idan kuwa hajji da umara zai yi a haxe sai ya ce,

“Labbaika Hajjan” (Ma’ana : Ya Allah na amsa maka da Hajji) wanda zai haxa hajji da umara sai ya ce, “Labbaikal Lahumma Hajjan Wa Umratan” (Ma’ana : Ya Allah na amsa maka hajji da umara”.

Saboda hadisin Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi ya ce – “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa, “Labbaika Umaratan Wa Hajjan”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

In maniyyaci bai ce komai ba to niyyarsa ta zuciya ta wadatar masa.

Ire-Iren Aikin Hajji

1 – Tamattu'i

Shi ne mutum ya yi niyyar umara a cikin watannin aikin hajji, ya gama umarar, ya fita daga cikin ihraminsa, sannan sai ya yi niyyar aikin hajji a wannan shekarar da ya yi umarar.

2 – Qirani

shi ne mutum ya yi niyyar hajji da umara a tare gabaxaya.

3 – Al-ifrad

Shi ne ya yi niyyar aikin hajji kawai.

Banbancin Da Yake Tsakanin Ire-Iren Aikin Hajji Uku

  At-Tamattu›i Al-Qirani Al-Ifrad
Yadda Ake Yi Yin Umara sannan yin aikin hajji Yin umara da hajji a haxe Yin Hajji Kawai
Ihrami Zai yi niyya sau biyu, ta farko umara, sannan ya cire ihraminsa bayan ya gama ta, sannan sai ya yi niyyar aikin hajji Zai yi niyya xaya tak don yin aikin hajji da umara Zai yi niyya xaya kawai ita ce ta hajji
Talbiyya Yayin ihramin farko zai ce, «Labbaika Umratan» sannan idan zai yi niyyar hajji sai ya ce, «Labbaika Hajjan» ko ya ce, «Labbaika umratan mutamatti›an biha ilal hajji». Yayin Ihrami zai ce, «Labbaika umratan wa hajjan». Yayin Ihrami zai ce, «Labbaika Hajjan»
Hadaya Hadaya ta wajaba a cikinsa Hadaya ta wajaba a cikinsa Babu Hadaya a cikinsa
Xawafi Xawafi biyu ne a cikinsa, xaya na umara, na biyu kuma na hajji Xawafi xaya ne a cikinsa na dole, shi ne xawafin hajji Xawafi xaya ne a cikinsa na dole, shi ne xawafin hajji
Sa›ayi A cikinsa akwai sa›ayi biyu, xayan na umara, xayan kuma na hajji Sa›ayi xaya ne a cikinsa kawai, shi ne sa›ayin hajji Sa›ayi xaya ne a cikinsa kawai, shi ne sa›ayin hajji

Talbiyya

Bayanin Talbiyya

Talbiyya

Ita ce, faxin Alhaji "Labbaikal Lahumma Labbaik, Labbaika La Sharika Laka Labbaik, Innal Hamda Wanni'imata Laka Wal Mulk, La Sharika Lak"

Saboda hadisin xan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, Haka Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ke talbiyya [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Ma’anar «Labbaikal Lahumma Labbaik» Shi ne na ansa maka, na ansa maka.

Talbiyya ta qunshi yabo da godiya ga Allah, na ansa wa umarninsa, da bayyana kaxaitar shi, da kuvuta daga shirka.

Hukuncin Talbiyya

Yin talbiyya sunna ce, namiji zai xaga muryarsa da ita, mace kuwa zata yi qasa-qasa da muryarta, don gudun fitina.

Lokacin Talbiyya Da Wuraren Da Ake Yin Ta

Maniyyaci zai fara talbiyya bayan sanya ihraminsa, ya yi ta yinta a kan hanyarsa. Ana qarfafa yin ta a wurare da yawa, daga cikinsu akwai :

Idan ya hau tudu, ko ya yi gangara, ko ya yi sallar farilla, ko idan dare ya yi, ko rana ta yi.

Zai daina yin talbiyyar umara idan ya ga ka’abah ya sumbaci Hajarul Aswad. A hajji kuwa zai daina talbiyya idan ya fara jifan wurin jifa na qarshe a ranar idi.



Tags: