Miqati

5243

Bayanin Miqati

Ma’anar Miqati A Larabci

Shi ne iyaka tsakanin abubuwa biyu

Ma’anar Miqati A Wurin Malamai

Abin da shari'a ta iyakance shi kuma ta sanya shi lokaci na wata ibada, wuri ne ko lokaci

Kashe-Kashen Miqati

Na xaya: Miqati na wuri

Miqatin na wuri

Su ne wuraren da shari›a ta sanya su don yin haramar aikin hajji daga wurin

Baya halatta ga wanda ya yi niyyar hajji ko umara ya wuce waxannan wurare sai da ihrami, su ne wurare guda biyar [Alwamaqit Wa Ab’adaha, Na Sheikh Abdallah Al-bassam, Majallar «Maj’ma’ul Fiqihi Al-islamiy» Adadi na 3 Juzu’i na 3 shafi na 1553] :

1 – Zul-hulaifa

wuri ne da yake kudu da Madinah, ana kiransa a yau da «Abyaru Aliyyu» tsakaninsa da Makkah kusan kilo mita 420 ne.

Shi ne miqatin Mutanen Madinah.

Zul-hulaifa

2 – Juhfah

Wani wuri ne kusa da garin Rabig, tsakaninsa da Makkah kusan kilo mita 186.

Shi ne miqatin mutanen Sham da Misra da Maroco.

Al-juhfah

3 – Yalamlam

Wani kwari ne babba a kan hanyar mutane Yemen zuwa Makkah, A yanzu a kiran wurin da Assadiyyah, tsakaninsa da garin Makkah kusan kilo mita 120 ne. Kuma shi ne miqatin mutanen Yemen.

Yalamlam

4 – Qarnal-Manazil

A yanzu a kiransa da «Assail-Alkabir» tsakaninsa da Makkah kusan kilo mita 75 ne.

Shi ne miqatin mutanen Najad da Xa’if, samansa wajen hanyar mutanen Xa’if vangaren Hada akwai wani wuri da ake kira «Wadi Mahram» dukkaninsu miqatin mutanen garin Najadu ne, da duk wanda ya biyo ta hanyar garin Xa’ifa.

Qarnal-Manazil

5 – Zatul-Irqi

A yanzu ana kiransa da «Addariba, ko Alkhuraibat» wuri ne da yake gabas da Makkah, tsakaninsa da Makkah kusan kilo mita 100 ne, amma yanzu wurin ba mutane.

Shi ne miqatin mutanen Iraqi, Iran, da garuwan da suke vangarensu.

Waxannan miqatan sun zo a hadisin Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya sanya wa mutanen Madinah Zul-hulaifa ya zama miqatinsu, mutanen Sham kuma Juhfah Mutanen Najadu Qarnal-Manazil Mutanen Yemen Yalamlamsannan ya ce, “Waxannan miqatinsu ne da wanda ya zo ta wajensu, wanda ba xan garin ba, wanda ya yi niyyar aikin hajji da umara Wanda yake gaba da su kuwa to miqatinsa daga inda ya tashi, har mutanen Makkah daga Makkah” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Zatul-Irqi kuwa ba a ambace ta ba a wannan hadisin da ya gabata. Umar xan Khaxxabi shi ne ya sanya ta [Bukhari ne ya rawaito shi].

Zatu-Irqin

Na biyu: Miqatin Lokaci

Miqatin Lokaci

Lokacin Aikin Hajji Da Umara

A – Lokacin ko zamanin aikin hajji

waxanda su ne Shawwal, Zul-qida, kwana goma daga Zul-hajj.

B – Lokacin ko zamanin umara

shi ne dukkan watannin shekara gaba xaya.



Tags: