Sallar Juma’a

42951

Hukuncin Sallar Juma’a

Sallar Juma’a wajibi ce a kan dukkan wani musulmi, baligi, mai hankali, wanda ba shi wani uzuri a kan barinta.

Abin da yake nuna haka shi ne :

1- Faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Ya waxanda suka yi imani idan an yi kiran sallah na ranar Juma’a to maza ku tafi zuwa ambaton Allah, ku bar ciniki” (Al-jum’a : 9).

2- Da faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Wallahi kodai wasu mutane su hanu ga barin juma’a, ko kuma Allah ya rufe zukatansu, sannan su zama cikin gafalallu” [Muslim ne ya rawaito shi].

Waxanda Juma’a Bata Wajaba A Kansu Ba

Juma’a bata wajaba a kan mace ba, da yaro, da matafiyi, da mara lafiyar da halarttar ta zai yi masa wahala, sai dai tana inganta daga wajensu, idan sun halacceta tare da sauran mutane ta isar musu, in kuma ba su hallaceta ba sai su yi sallar azzahar.

Maras lafiya
Matafiyi
Mace
Yaro

Falalar Ranar Juma’a

Ranar Juma’a ita tafi dukkan kwanakin sati falala, Allah Maxaukakin Sarki ya kevance ta ga wannan al’umma, bayan sauran al’ummu sun kasa gane ta. Falalar wannan rana ta zo a cikin hadisai da yawa, daga cikinsu :

1- Faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Mafi alherin yini da rana ta vullo a cikinsa shi ne ranar Juma’a, a cikinta ne aka halicci Adam, a cikinta ne aka shigar da shi Aljannah, a cikinta ne aka fitar da shi daga cikinta” [Muslim ne ya rawaito shi].

2- An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda duk ya yi wanka, sannan ya je Juma’a, ya sallaci abin da aka qaddara masa (na nafila) sannan ya yi shiru har (liman) ya gama huxubarsa, ya yi sallah tare da shi, an gafarta masa abin da ke tsakanin wannan rana da juma’ar da zata zo, da qarin kwana uku” [Muslim ne ya rawaito shi].

3- An karvo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Salloli biyar, da juma’a zuwa juma’a, da Ramadan zuwa Ramadan, suna kankare abin da yake tsakaninsu idan an nisanci manya-manyan zunubai” [Muslim ne ya rawaito shi].

Sharuxxan Ingancin Sallar Juma’a

1- Lokaci : Sallar juma’a bata inganta kafin lokacinta, ko bayan fitar lokacinta, kamar sauran sallolin da aka wajabta. Lokacinta shi ne lokacin azzahar.

2- Jama’a su halarce ta : Bata inganta daga mutum xaya. Mafi qarancin jama’ar mutum uku.

3- Zama a Gari : shi ne zama a alqarya mai gidaje ginannu da bulo, ko makamancin haka na abubuwan da aka saba gini da su, ya zama ba a tashi daga wannan gari da sanyi ko zafi.

Amma waxanda suke cikin hemomi, suna tashi daga nan zuwa can, waxannan sallar juma’a bata wajaba a kansu ba, sai dai ta inganta daga gare su idan suka yi ta.

4- Huxubobi biyu su gabace ta, saboda tabbatar Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) akan yin su.

Mazauna qauyukan (da suke tashi) juma’a bata inganta a wurinsu.
Lokacin Sallar Juma’a
Ana sallatar Juma’a a cikin jam’i

Siffar Yadda Ake Sallar Juma’a

Sallar Juma’a raka’a biyu ce, ana bayyana karatu a cikinsu. A sunnah ne a karanta suratul Juma’a bayan an karanta fatiha a raka’ar farko, a raka’a ta biyu kuma a karanta suratul Munafiquun bayan fatiha, ko kuma a karanta suratul A’ala a farko, a ta biyu suratul Gashiyah [Muslim ne ya rawaito shi].

Huxobobi Biyu

Hukuncin Huxubobi Biyu

Yin huxobobi biyu wajibi ne, kuma sharaxi ne na ingancin sallar juma’a, ana yin su da larabci idan yawancin waxanda suke nan suna fahimtar larabci, suna gane shi a dunqule, ana son yi da larabci ne don kwaxaitar da su a kan koyon larabci, da kuma rashin savawa shiriyar Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) .

Idan kuwa yawancin waxanda suke wurin basa fahimtar larabci, to babu laifi a yi su da waxansu yaruka daban.

Saboda asali a huxuba shi ne karantarwa da koyarwa da nusarwa, ba wai kawai yin ta ba, amma tare da kiyaye kawo ayoyi da larabci sannan a fassara in zai yiwu

Mustahabban Huxuba (Abubuwan Da Ake So A Huxuba)

1- Huxuba akan minbari

2- Sallamar mai huxuba ga mutane yayin da ya hau minbari

3- Rabewa tsakanin huxubobi biyu da xan zama kaxan

4- Taqaita huxubobin biyu

5- Yin addu’a a cikinsu

Abubuwan Da Huxuba Take Cika Da su

Huxubar juma’a bata da wasu rukunai. tana samuwa da duk abin da ake cewa huxuba, sai dai yana cikin cikarta mai huxuba ya yi abubuwan da za su zo :

1- Godiya ga Allah

2- Kalmar Shahada biyu

3- Salati ga Annabi ( صلى الله عليه وسلم )

4- Wasiyya da tsoron Allah

5- Karanta wani abu daga cikin Alqur’ani

6- Wa’azi

Abin Da Aka Hana Yi A Sallar Juma’a

1- Haramun ne yin magana a lokacin da liman yake huxuba, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “Idan ka ce wa abokinka ranar juma’a “yi shiru” alhali liman yana huxuba, to ka yi maganar banza” [Bukhari ne ya rawaito shi].

2- An karhanta tsallaka mutane, sai dai in liman ne, ko kuma zai tsallaka zuwa wurin da ba kowa.

Riskar Juma’a

Wajibi a kan musulmi ya yi gaggawa zuwa sallar juma’a, ya tafi da wuri, idan ya makara, amma ya samu ruku’u tare da liman a raka’a ta biyu, sai ya cika sallarsa ta juma’a, idan kuwa bai samu raka’a ta biyu ba, to zai cika sallarsa ne azzahar.

Hakanan wanda juma’a ta wuce shi saboda barci, ko wani abun, to zai sallace ta ne azzahar, raka’a huxu.

Abin Da Ake So Ranar Juma’a

1- Karanta suratul Kahfi ranar Juma’a, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “wanda ya karanta suratul kahfi ranar juma’a, za a haskaka masa tsakanin juma’a guda biyu” [Hakim ne ya rawaito shi].

2- Yawaita salati ga Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) . An karvo daga Abu Mas’ud Al-ansariy – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Ku yawaita salati ranar juma’a, babu wani da zai yi min salati ranar juma’a face sai an bijirar min da salatinsa” [Hakim ne ya rawaito shi].

3- Yin wanka da sanya turare, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Mutum ba zai yi wanka ba ranar juma’a, ya yi tsarki daidai gwargwado, ya shafa mai daga man da yake da shi, ko ya sanya turaren gidansa, sannan ya fita (zuwa masallaci) bai raba tsakanin wasu mutane biyu ba, sannan ya sallaci abin aka rubuta masa (daga nafila), sannan ya yi shiru idan liman yana magana, face sai an gafarta masa abin da yake tsakanin wannan juma’a da wata juma’ar mai zuwa” [Bukhari ne ya rawaito shi].

Mas’aloli A Kan Sallar Juma’a

1- Abin da yake sunna shi ne minbari ya zama mataka uku ne, koyi da minbarin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) .

Minbari mai matakala uku

2- Ba sunnah ba ne abin da ake cewa suratul juma’a, wato masallata su zauna kafin juma’a suna jin karatun wani mai karatu, yana karanta musu ayoyin Alqur’ni kafin sallar juma’a.

har zuwa a yi kiran juma’a, ko kuma rera waqoqi da yin zikiri da sauti xaya da lasifika.

3- Idan mai sallah ya zo liman yana huxuba, zai yi nafila biyu gajeru kafin ya zauna, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Idan xayanku ya zo ranar juma’a, liman yana huxuba, to ya yi raka’a biyu, ya taqaita su”[Ibnu Khuzaimah ne ya rawaito shi].

4- Mai huxuba zai yi addu’a da xaga xan yatsansa manuniya, ba zai xaga hannayensa ba in yana addu’a sai dai in roqon ruwa yake, ko kuma addu’ar neman a daina ruwa.

An karvo daga Hussain xan Abdur-Rahman – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Na ga Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana huxuba, idan yana aduu’a zai ya yi nuni da xan yatsansa manuniya” [Ahmad ne ya rawaito shi].

5- Sallar juma’a bata da wata nafila da ake yin ta gabaninta, kaxai ana son yin nafilfili kafin kiran sallah, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) : “ Mutum ba zai yi wanka ba ranar juma’a, ya yi tsarki daidai gwargwado, ya shafa mai daga man da yake da shi, ko ya sanya turaren gidansa, sannan ya fita (zuwa masallaci) bai raba tsakanin wasu mutane biyu ba, sannan ya sallaci abin aka rubuta masa (daga nafila), sannan ya yi shiru idan liman yana magana, face sai an gafarta masa abin da yake tsakanin wannan juma’a da wata juma’ar mai zuwa” [Daarimiy ne ya rawaito shi]

6- Ana sallatar nafilar bayan juma’a raka’a biyu, saboda abin da xan Umar ya rawaito ya ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana yi raka’a biyu bayan juma’a a gidansa” [Jama’a ne suka rawaito shi].

Ko a yi raka’a huxu, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Duk wanda zai yi sallah bayan juma’a, to yaa yi raka’a huxu” [Muslim ne ya rawaito shi]. Yin ta a gida shi ya fi.

7- Idan idi da juma’a suka haxu to abin da ya fi shi ne mutum ya sallaci idin da juma’ar, in kuma ya yi sallar idi to ba makawa ya yi sallar azzahar.

An yi rangwame ga mutane garuruwa masu nisa idan sun sallaci idi, kada su dawo zuwa sallar juma’a.

An karvo daga Iyas xan Abi Ramla Ash-shamiy ya ce, “Na sami Mu’awiya ya tambayi Zaid xan Arqam ya ce masa, “Ka halacci haxuwar idi biyu (Juma’a da idi) tare da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ? sai ya ce, “Eh, ya sallaci idi da farkon rana, sannan ya yi rangwame akan (zuwa) juma’a, ya ce, wanda ya ga damar ya yi juma’a to ya yi”[Ahmad ne ya rawaito shi]Tags: