Lailatul Qadari

7638

Me Ya Sa Aka Kira Shi Da Lailatul Qadri

1 – An ce, saboda girmamawa (saboda kalmar Qadru a larabci tana nifin girma) kamar faxin Allah Maxaukakin Sarki “Ba su girmama Allah iyakar girmamawa ba”. (Al-An’am : 91)

Abin da ake nufi, wannan dare ne mai girma, saboda Alqura’ni ya sauka a cikinsa, da kuma abin da yake faruwa na saukar Mala’iku da Albarka da Rahama da gafara a cikinsa”.

2 – Wasu kuma suka ce, Alqadru, yana nufin quntatawa, kamar yadda Allah ya yi amfani da wannan kalmar da wannan ma’ana inda yake cewa “Wanda aka quntatawa arzikinsa ya ciyar daga abin da Allah ya ba shi”. (Axxalaq : 7)

Abin da ake nufi da quntatawa a cikin wannan dare, shi ne voye daren da aka yi, ba a bayyana shi ba.

3 – Wasu suka ce, “Alqadru a nan, yana da ma’anar “Alqadaru” wato qaddara, saboda abin da ake qaddara wa na shekara cikin wannan dare, don Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “A cikin wannan dare ne ake rarrabe dukkan wani lamari hukuntacce. (Addukhan : 4)[Fathul- Bari (4/255)]

Falalar Daren Lailatul Qadari Da Matsayinsa

1 – A Cikinsa Ne Aka Saukar Da Alqur’ani

Allah ya ce, “Haqiqa Mun saukar da shi a cikin daren Lailatul Qadri” (Alqadri : 1).

2 – Ya Fi Wata Dubu

Allah ya ce, “Daren Lailatul Qadari ya fi wata dubu alheri” (Alqadri : 3).

Ma’ana aiki a cikin wannan dare ya fi aikin wata dubu ba a daren Lailatul Qadari ba.

3 – Mala’ika Jibril Da Sauran Mala’iku Suna Sauka A Cikinsa

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Mala’iku da Mala’ika Jibrilu suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu daga kowane lamari” (Alqadri : 4).

An kavo daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Daren Lailatul Qadari shi ne daren ashirin da bakwai ko ishirin da tara. Mala’iku a wannan daren sun fi yawan tsakuwa a bayan qasa” [Ibn Khuzaima ne ya rawaito shi].

4 – Dare Mai Aminci A Cikinsa

Allah Mai Girma Da Buwaya ya ce, “Aminci ne a cikinta har zuwa vullowar alfijir”. (Alqadri : 5)

Ma’ana dukkan wannan dare alheri ne, babu wani sharri a cikinsa tun daga farkonsa har zuwa vullowar alfijir.

5 – Dare Ne Mai Albarka

Allah ya ce, “Haqiqa mun saukar da shi a cikin dare mai albarka. Haqiqa mu masu gargaxi ne”. (Addukhan : 3).

Abdullahi xan Abbas ya ce, “Yana nufin daren lailatul Qadri”.

6 – A Cikinsa Ake Qaddara Dukkan Abubuwan Shekara

Allah ya ce, “A cikinsa ake rarrabe kowanne lamari abin hukuntawa” (Addukhan : 4).

7 – Wanda Ya Yi Qiyamullaili Yana Mai Imani Da Neman Lada To Za A Gafarta Masa Abin Da Ya Gabata Na Zunubinsa

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda duk ya yi tsayuwar daren Lailatul Qadri yana mai imani da neman lada, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Wane Dare Ne Lailatul Qadri

Allah ya voye wannan dare don musulmi ya yi qoqari da himma a goman qarshe ta Ramadan, musamman ma a dararen da suke mara, waxanda su ne daren 21, 23, 25, 27, 29, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Ku kintaci daren Lailatul Qadri a cikin marar goman qarshe ta Ramadan” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Wasu malamai sun yi bayanin cewa daren Lailatul Qadri yana yawo a tsakanin waxannan darare (Wata shekarar wannan, wata shekarar wancan) saboda a yi aiki da dalilan da suka zo a kan haka baki xaya.

Ayyukan Da Ake Son Yi A Daren Lailtul Qadri

1 – I'itikafi

Ana yinsa ne a goman qarshe a Ramadan, ba sai a daren Lailatul Qadri kaxai ba. An karvo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana yin I’itikafin kwanaki goma na qarshe a Ramadan” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

2 – Tsayuwa a wannan dare don imani da neman lada

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda ya yi tsayuwa daren Lailatul Qadri yana mai imani da neman lada, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

3 – Addu'a

An karvo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, na ce, ya Rasulallahi, idan na dace da daren Lailatul Qadri, me zan yi addu’a da shi? Sai ya ce, ki ce, “Allahumma Innaka Afuwwun Karimun Tuhibbul Afwa Fa’afu Anni” Ma’ana “Ya Allah kai mai afuwa ne mai karamci, kana son afuwa, ka yi min afuwa” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Alamomin Daren Lailatul Qadri

1 – Dare Ne Mai Haske, Babu Zafi Ko Sanyi A Cikinsa

An karvo daga Jabir xan Abdullahi – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Haqiqa ni an nuna min daren Lailatul Qadri, sannan an mantar da ni shi, yana goman qarshe na Ramadan, dare ne babu sanyi ko zafi a cikinsa, kuma mai haske ne, ba zafi ba sanyi (mai cutarwa a cikinsa)” [Ibn Khuzaima ne ya rawaito shi].

2 – Rana Tana Fitowa Da Safiyar Daren Fara Tas Ba Haske Tare Da Ita.

Yayin da aka tambayi Ubayyu xan Ka’abu – Allah ya yarda da shi – a kan alamomin daren Lailatul Qadri, sai ya ce, “Alamar da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ba mu labari ita ce, rana tana vullowa a wannan rana babu haske tare da ita” [Tirmizi ne ya rawaito shi].Tags: