I’itikafi

4906

Bayanin menene I'itikafi

Ma’anar I’itikafi a larabci

Shi ne : lizimtar wani abu da tsare kai a kansa

Ma’anar I’itikafi a shari’a

Shi ne : Lizimtar masallaci don bauta wa Allah Maxaukakin Sarki

Bayanin Shar’ancin I’itikafi

I’itikafi yana cikin ayyuka masu falala, da biyayya ga Allah mai girma. An karvo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana I’itikafin kwana goman qarshe na Ramadan, har Allah ya karvi ransa” [Bukhari ne ya rawaito].

An shar’anta mana I’itikafi mu da waxanda suke gabace mu. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Mun yi wasiyya ga Ibrahim da Isma’ila su tsarkake xakina saboda masu xawafi da I’itikafi da masu ruku’I da sujjada” (Al-baqara : 125).

Hukuncin I’itikafi

I’itikafi sunna ne a kowane lokaci, amma wanda yafi falala shi ne na goman qarshe a cikin Ramadan, saboda Manzon Alah ( صلى الله عليه وسلم ) ya dawwama a kan yin I’itikafin goman qarshe ta Ramada [Zadul Ma’ad]

Sharuxxan I’itikafi

1 – Niyya

Mai I’itikafi zai yi niyyar lizimtar masallaci don kusanci da bautawa Allah. Saboda Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Dukkan ayyuka suna karvuwa ne da niyya” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

2 – Masallacin Da Zai I’itikafin A Cikinsa Ya Zama Na Juma’a Ne

Ma’ana ya zama masallaci ne da ake sallar juma’a a cikinsa, duk mutanen gari gabaxaya suna taruwa a cikinsa. Ba masallacin wata unguwa kaxai ba.

3 – Tsarki Daga Babban Kari

I’itikafin mai janaba ba ya inganta, haka ma mai haila, da mai jinin biqi, saboda waxannan ba ya halatta su zauna a masallaci.

Azumi Ba Sharaxi Ba Ne A I'itikafi

Ba a lissafa azumin a cikin sharuxxan I’itikafi, saboda abin da aka rawaito daga xan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, Umar ya tambayi Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Na yi bakancen a Jahiliyya cewa zai I’itikafin dare xaya a masallacin Harami (makka) sai Manzon Allah ya ce, “Cika Bakancenka” [Bukhari ne ya rawaito shi].

To da azumi sharaxi ne da I’itikafin dare xaya bai inganta ba, saboda ba a azumi da daddare. Hakanan ya tabbata “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi I’itikafin goman farko a watan Shawwal” [Muslim ne ya rawaito shi],

a cikin waxannan kwanaki kuwa akwai ranar idi, wadda ba ya halatta a yi azumi a cikinta, kuma azumi da I’itikafi kowane ibada ce mai zaman kanta, babu sharaxin sai an samu xaya sannan a samu xayar.

Lokacin Yin I’itikafi

Ya inganta a yi I’itikafi a kowane lokaci, sai dai abin da ya fi, kada I’itikafi ya gaza kwana xaya, domin ba a samo daga Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) ba ko wani daga cikin sahabbansa ya yi I’itikafin qasa da kwana xaya.

I’itikafin Kwana Goman Qarshe A Ramadan

-Wannan lokaci shi ya fi dukkan lokutan I’itikafi falala, saboda abin da ya tabbata daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana I’itikafin kwana goma na qarshe a Ramadan, har Allah ya karvi ransa” [Bukhari ne ya rawaito shi].

-Wanda ya yi niyyar I’itikafin goman qarshe na Ramadan, sai ya yi sallar asuba a wayewar garin ishirin da xaya ga watan Ramadan a masallacin da yake so ya yi I’itikafi a cikinsa.

An karvo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana yin I’itikafi a kowane Ramadan. Idan ya yi sallar asuba sai ya shiga wurin da zai yi I’itikafin a cikinsa” [Bukhari ne ya rawaito shi]

-I’itikafi yana qarewa da faxuwar ranar qarshe daga Ramadan. Amma abin da ya fi shi ne a fita daga I’itikafin a wayewar ranar idi, saboda shi ne abin da ya tabbata daga magabata.

Hikimar Yin I’itikafi :

Hikimar yin I’itikafi ita ce yankewa ga barin duniya, da shagalta da ita da ma’abotanta, da kuma maida hankali ga ibada, don haka ya dace ga mai I’itikafi ya shirya zuciyarsa don haka

Abin Da Ya Halatta Mai I’itikafi Ya Yi

1 – Fita daga cikin Masallaci saboda yin abin da ba makawa sai an yi shi, kamar fita don cin abinci da shan ruwa, idan babu wanda zai kawo masa su, da fita don biyan buqata (bayan gida ko bawali).

Saboda da abin da ya tabbata daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance idan yana I’itikafi yana kusanto min da kansa in taje masa shi, kuma ya kasance ba ya shigo wa gida sai don wata buqatar xan adam” [Muslim ne ya rawaito shi].

2 – Taje kai da gyara shi, saboda hadisin da ya gabata.

3 – Yin magana da mutane cikin abin da yake da amfani, da tambayar halin da mutane suke ciki, sai dai kada a yawaita hakan, saboda zai savawa manufar I’itikafi.

4 – Yan uwa da makusanta su ziyarci mai yin I’itikafi, shi kuma ya fito don raka su. An karvo daga Safiyya ‘yar Huyai – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) yana I’itikafi, sai na zo masa ziyara a wani dare, na yi magana da shi, sannan sai na tashi, don in tafi, sai ya tashi ya raka ni” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Abubuwan Da Suke Vata I’itikafi

1 – Barin masallaci da gangan ba tare da wata buqata ba, koda kuwa na xan lokaci kaxan ne.

Saboda abin da ya tabbata daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance ba ya shigo wa gida sai don wata buqatar xan adam” [Muslim ne ya rawaito shi].

Kuma saboda barin masallaci ya savawa zama a masallaci, wanda rukuni ne na I’itikafi.

2 – Saduwa da mace, koda kuwa da daddare ne,

saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki “Kada ku rungumi matanku alhali kuna I’itikafi a masallaci” (Al-baqara : 187).

Kuma yana shiga cikin hukuncin saduwa, fitar da maniyyi tare da jin daxi, kamar yin wasa da hannu, da rungumar mace.

3 – Yin niyyar yanke I'itikafi

Idan musulmi ya yi niyyar I’itikafin wasu kwanaki qididdigaggu, amma sai ya yanke I’itikafin, to ya halatta ya rama shi, saboda abin da ya tabbata daga A’isha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance idan zai yi I’itikafi, yana yin sallar asuba, sannan ya shiga wurin I’itikafinsa. Ya yi umarni a kafa masa rumfa, yana so ya yi I’itikafin goman qarshe na Ramadan, sai matarsa Zainab ta yi umarni a kafa mata rumfarta, aka kafa mata, sauran matan Annabi ( صلى الله عليه وسلم ) su ma suka yi umarni aka kafa musu rumfunansu. Da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi sallar asuba, ya duba sai ya ga an kafa rumfuna, sai ya ce, “aikin alheri kuke nufi?” Sai ya yi umarni a cire rumfarsa, ya fasa yin I’itikafi a watan Ramadan, ya yi I’itikafin a goman farko a cikin watan shawwal”. A wata riwaya “goman qarshe ta Shawwal” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

4 – Mai I’itikafi ba ya zuwa duba marar lafiya, ba ya halartar jana’iza.

Ya dukufa a kan bautawa Allah a wurin I’itikafinsa.Tags: