• wannan shine aikin farko kuma mafi girma wanda ya karaxe hukunce-hukunce na fiqihu da babu wani gida na musulmi mai wadatuwa daga barinsa. • cikakkiyar manhaja ce ta koyarda ibada ga xaixaikun mutane, da wajen taruwan mata da qungiyoyi da cibiyoyi da makarantu da sauransu. • yana alaqanta mutane kai tsaye da alqur'ani da sunnah ta mafi sauqin hanya da hotuna. • yana sauqaqe hanyoyin koyo da fahimta ga dukkan musulmi, domin aiki ne da aka yishi a zamanance. • ana kwatanta ayyukan ne a aikace quru-quru, saboda faxin Manzon Allah s.a.w: "kuyi sallah kamar yadda kuka gani ina sallah". • kowane darasi yana xauke da hotuna masu kwatanta aikin a aikace, bugu-da-qari kuma ga bidiyo. • an fassara shi zuwa yaruka 14, wanda sama da mutum biliyan biyar ke magana dasu a faxin duniya. • littafin na goye da duniyar fiqihu, wadda ta qunshi sama da bidiyo hamsin , da sautuka da littafai birjik masu dangantaka da fiqihu.