Muna taya ka murnar kamala rijistar Bita a kan hukunce-hukuncen tsarki a cikin hotuna

103

Muna taya ka murnar kamala rijistar Bita a kan hukunce-hukuncen tsarki a cikin hotuna

الطهارة والمياه

Allah Mai Girma da Daukaka Yana cewa:

{قُلْ هَلْ يَسْتَوِي الَّذِينَ يَعْلَمُونَ وَالَّذِينَ لا يَعْلَمُونَ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُولُو الْأَلْبَاب}

"Ka ce dasu shin wadan da suke da Ilimi, za su yi daidai da wadan da ba da Ilimi?

(Suratul Zumar, aya ta 9)

Muna taya ka murnar kamala rijistar Bita a kan hukunce-hukuncen tsarki a cikin hotuna. Allah Ya datar da kai, Ya rubuta maka lada, kuma muna maka bishara da fadin Manzin Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: ((Duk wanda ya kama hanyar neman Ilimi, to, Allah Zai saukaka masa hanyar zuwa Aljannah)). Muslim ya ruwaito.
((Duk wanda ya yi nuni zuwa wani aikin alkhairi, to, yana da lada irin ladan wanda ya aikata aikin)).  

'Yan'uwa masu albarka, ku yaɗa wannan aikin alkhairi, ku tuttura sanarwar wannan Bita a kafafen sada zumunta na zamani kamar Telegram, WhatsApp, Facebook, Twitter, Instagram da sauran su, kuma ku ƙwaɗaitar da mutane su yi rijistar a ciki ta hanyar waɗan nan shafuka na yanar gizo da ke tafe:

Shafin yanar gizo na Telegram

Shafin yanar gizo na Bita

Shafin yanar gizo na rijista

Shafin yanar gizo na Fiƙihun Ibadu a cikin hotuna

Tsare-tsare da lokutan Bitar:

Za a fara wannan Bita ne ranar 10 ga watan Yuni (June) a cikin kwanaki shida, za a turo Darussan a cikin waɗan nan kwanakin.

Jarabawa kuma za a fara ta 16 ga watan Yuni (June) In Allah Ya so Ya amince, za a tura tambayoyi da karfe biyar agogon Makkah (Karfe uku agogon Nigeria da Niger).

Za a tura sakamakon jarabawa bayan an gama jarabawar.

Duk wanda ya samu 70% zai samu certificate.

Duk wanda ya samu 95% za a tura mishi saƙo na musamman domin godiya.

Yin irin waɗan nan karatuttukan saboda Allah (IKHLASI) ya kan sa su zama cikin jerin gwanon ayyuka masu falala a wurin Allah.

Darussan Bita:

Bitar za ta gudana ne cikin kwanaki shida, kuma darussa goma sha ɗaya ne, kuma za mu turo muku Darussan da wuri don ku samu lokacin yin Muraji'ar Karatuttukan domin jarabawa, kuma ka da lokaci ya ƙure muku, waɗan nan su ne Darussan Bita a kan Hukunce-Hukuncen tsarki a ciki a kwai darasi 11, abin nema shi ne ku karanta kowane darasi kuma ku kalli bidiyonshi.

Darasi na farko 1:Tsarkin ruwa a Musulunci

Karanta

Kalla

Darasi na biyu 2: Hukunce-hukuncen najasa

Karanta

Kalla

Darasi na uku 3: Sauran ruwa (Wanda a ka yi amfani dashi)

Karanta

Kalla

Darasi na hudu 4: Kwanuka

Karanta

Kalla

Darasi na biyar 5: Biyan bukata

Karanta

Kalla

Darasi na shida 6: Sunnonin fitira

Karanta

Kalla

Darasi na bakwai 7: Alwala

Karanta

Kalla

Darasi na takwas 8: Shafa a kan huffi da safa da karan dauri da makamantansu.

Karanta

Kalla

Darasi na tara 9: Wanka

Karanta

Kalla

 Darasi na goma  10: Taimama 

Karanta

Kalla

DARASI na goma sha daya 11: Haila da jinin cuta da na biki.

Karanta

Kalla

Bahasa-bahasa Daurah :


 
 
Telegram - Apps on Google Play دورة أحكام الطهارة المصورة